Bayanai sun nuna cewa, Marigayi Ibrahim Khalil Dan Shagamu, mai sharhi a kafafen sada zumunta a jihar Kano, ya taba bayyana cewa ana yi masa barazanar kisa makonni kadan kafin a kashe shi a gidansa da ke Gaida, Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.
Dan Shagamu, mai shekaru 54, ya roki Gwamnatin Jihar Kano, Sarkin Kano da rundunar ‘yan sanda da su shiga tsakani, yana zargin cewa wasu makwabtansa na ci gaba da tsangwamarsa tare da yi masa barazana.
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce yana bukatar taimakon gwamnan Kano, Sarkin Kano da ‘yan sanda saboda yana fuskantar barazanar kisa daga makwabtansa.
Ya kuma zargi wasu yara da ke unguwar da jifan gidansa da duwatsu, lalata talabijin dinsa da kuma taruwa a wajen gidansa suna zaginsa.
A cewarsa, ya kai rahoton lamarin ga shugaban unguwar Gaida, wanda daga bisani ya tura batun zuwa shugaban Ja’en, amma matsalar ba ta samu mafita ba.
Dan Shagamu ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikin makwabtansa sun san da barazanar da ake yi masa kuma sun hada baki a kansa.
Ya kuma wallafa wani bidiyo da ke nuna wasu yara a wajen gidansa, inda ya ce an ji suna yi masa barazanar kashe shi.
Wannan gargadi da ya taba yi ya sake daukar hankalin jama’a bayan rasuwarsa a safiyar Laraba.
‘Yan uwansa sun ce wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidansa tare da kashe shi.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan, yayin da bincike ke ci gaba da gudana.
Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce binciken farko bai nuna cewa kisan yana da alaka da ayyukan Dan Shagamu a kafafen sada zumunta ba.
A cewar kakakin ‘yan sandan, binciken farko ya nuna cewa lamarin na iya kasancewa sakamakon abin da ya kira “tsananin hassada da kiyayya daga makwabta.”
Dan Shagamu, wanda ya yi suna a karkashin sunan Dan Shagamu International, ya kasance yana wallafa bidiyoyi da sharhi kan siyasa, addini da al’amuran al’umma.
Ya kasance mai tsananin sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sannan ya yi amfani da shafinsa wajen tallata wasu ‘yan siyasa na adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, wanda ya taba bayyana a matsayin “Shugaban Kasa mai zuwa.”
Sharhinsa ya kuma shafi batutuwan addini da rikice-rikicen da suka shafi wasu malaman addinin Musulunci a Kano da sauran batutuwan da suka shafi al’umma.
Yanzu dai rokon da Dan Shagamu ya yi a bainar jama’a na neman kariya daga barazanar da ya ce yana fuskanta daga makwabtansa ya sake daukar sabon salo bayan kashe shi.
Hukumomi na ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya jawo kisan da kuma wadanda ke da hannu a lamarin.
Source: Dailytrust

0 Comment about the Post: