Thursday, August 27, 2026

Yadda Hotunan Tauraron Dan Adam Suka Bayyana Mummunar Barnar Ambaliyar Ƙasar Nepal da Yankin Tibet na ƙasar China.

Yadda Hotunan Tauraron Dan Adam Suka Bayyana Mummunar Barnar Ambaliyar Ƙasar Nepal da Yankin Tibet na ƙasar China.

Akalla mutane 359 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da ake ci gaba da neman sama da 1,300 a Nepal da yankin Tibet na ƙasar China, bayan mummunar ambaliyar ruwa da rushewar kankara ta haddasa a tsaunukan Himalaya.

Lamarin ya faru ne ranar Laraba, lokacin da wani babban yanki na kankara da duwatsu ya rabu a wani wuri mai tsayi a yankin Tibet, lamarin da ya toshe kogin Lhende na wani lokaci. 
Bayan katangar ta rushe, wata babbar kwararar ruwa mai dauke da laka da duwatsu da tarkace ta mamaye garuruwa da kauyuka da ke kusa da iyakar Nepal da Tibet.

Gundumar Rasuwa da ke arewacin Nepal na daga cikin wuraren da suka fi fama da barnar. Ambaliyar ta lalata gidaje da cibiyoyin samar da wutar lantarki da hanyoyi da gadoji, yayin da garuruwan Timure da Syapru Besi suka fuskanci mummunar barna.

Mahukunta sun ce akalla gadoji 19 da kusan kilomita 40 na hanyoyi sun lalace, lamarin da ya kara wahalar da aikin ceto. Kakakin rundunar ‘yan sandan Nepal, Abi Narayan Kafle, ya gargadi cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa yayin da jami’an ceto ke ci gaba da neman wadanda suka tsira.

Hotunan tauraron dan adam da aka dauka kafin da bayan ambaliyar sun nuna girman barnar, inda aka ga gine-gine da hanyoyi sun shafe, yayin da manyan sassan garin Syapru Besi suka nutse cikin laka.

A Tibet kuma, yankin Gyirong Port ya fuskanci mummunar ambaliyar laka. Kafofin yada labaran kasar China sun ruwaito cewa laka ta kai zurfin sama da mita 1.5 a wasu wurare, yayin da wasu sassan hanyoyi suka nutse karkashin tarkace masu zurfin sama da mita biyu.

Da farko an yi zargin cewa girgizar kasa mai karfin 4.4 ce ta haddasa lamarin. Sai dai Hukumar Binciken Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) ta bayyana daga baya cewa girgizar da aka samu ta samo asali ne daga zaftarewar kasa, wadda ta haifar da girgizar da ta yi daidai da makamashin 5.2.

Ruwan ambaliyar ya bi daga kogin Lhende Khola zuwa kogunan Bhotekoshi da Trishuli. Jami’an Nepal sun ce matakin ruwan kogin Trishuli ya tashi da kusan mita tara cikin mintuna 30 kacal.

Ambaliyar da tarkacen laka sun kuma isa yankunan da ke nesa daga inda lamarin ya fara. An gano gawarwaki a wasu gundumomi da suka hada da Gorkha da Tanahunda Chitwan da Nawalparasi.

Kungiyoyin ceto na ci gaba da neman mutanen da suka bace, amma lalacewar hanyoyi da gadoji, tare da yanayin tsaunukan Himalaya mai wahala, na kara kawo cikas ga ayyukan ceto da agajin gaggawa.

0 Comment about the Post: