Saturday, August 8, 2026

An gano gawarwakin mutane 19 a ƙarƙashin baraguzan ginin Gaza

An gano gawarwakin mutane 19 a ƙarƙashin baraguzan ginin Gaza

Ma’aikatan agaji da rundunar kare fararen hula a Gaza sun gano gawarwakin Falasɗinawa 19, mafi yawansu mata da yara, a ƙarƙashin baraguzan wani ginin gidaje da ya rushe a Gaza.

A cewar Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza, an kammala aikin gano gawarwakin ne ranar Asabar, bayan shafe kwanaki huɗu ana gudanar da aikin bincike a ginin Karam da ke yammacin birnin Gaza.

Jami’ai sun ce aikin ceto da kwashe gawarwakin na fuskantar matsaloli saboda ƙarancin manyan injinan da ake buƙata wajen ɗaga manyan tarkacen siminti da suka ruguje.

A sakamakon haka, ma’aikatan kare fararen hula suna amfani da kayan aiki na yau da kullum da kuma ƙoƙarin hannu wajen neman gawarwakin mutanen da suka makale a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

Mohammed Abu Dan, wanda ke kula da ayyukan kwashe gawarwakin, ya ce bayan kammala aikin a ginin Karam, ƙwararrun ma’aikatan lafiya da jami’an kare fararen hula za su koma wani sabon wuri a Gaza City domin ci gaba da aikin neman waɗanda suka rasa rayukansu.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce akwai fiye da mutane 8,000 da har yanzu ake nema a ƙarƙashin baraguzan gine-gine a faɗin yankin.

Ta kuma bayyana cewa tun bayan fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar 11 ga Oktoba na shekarar da ta gabata, an kashe aƙalla mutane 1,254, yayin da wasu 4,121 suka jikkata, sannan aka gano gawarwakin mutane 804 daga ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

A cewar ma’aikatar, adadin mutanen da aka kashe tun bayan fara yaƙin a watan Oktoban 2023 ya haura 73,300, yayin da fiye da 174,000 suka jikkata.

Wannan aikin ceto ya zo ne kwanaki kaɗan bayan gudanar da jana’izar mutane 112 a birnin Gaza, waɗanda gawarwakinsu aka gano a ƙarƙashin baraguzan wani ginin gidaje da aka lalata a unguwar Sabra a watan Nuwamban 2023.

0 Comment about the Post: