Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana Alhamis, 16 ga Yulin 2026, a matsayin ranar farko na watan Safar 1448AH, bayan da ba a ga jinjirin watan Safar a fadin Najeriya ba.
Sanarwar ta fito ne cikin wata takarda da Kwamitin Harkokin Addini na Majalisar Masarautar Sakkwato ya fitar, mai dauke da sa hannun Shugaban kwamitin, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato.
A cewar sanarwar, Kwamitin Ganin Wata na Kasa tare da kwamitocin jihohi ba su samu wani sahihin rahoto da ya tabbatar da ganin jinjirin watan Safar a ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga Muharram 1448AH ba.
Saboda haka, an ayyana Laraba, 15 ga Yulin 2026, a matsayin cikar kwanaki 30 na watan Muharram, kamar yadda tsarin kalandar Musulunci ya tanada.
Bisa wannan rahoto, Sarkin Musulmi ya amince da kammala watan Muharram tare da ayyana Alhamis, 16 ga Yulin 2026, a matsayin ranar farko na watan Safar 1448AH.
Sanarwar ta zama jagora ga al'ummar Musulmi a Najeriya wajen gudanar da ibadu da sauran al'amuran addini da suka shafi kalandar Hijira.

0 Comment about the Post: