Thursday, July 30, 2026

Mata Sun Fi Maza Yawa a jadawalin Sabbin Masu Rajistar Katin Zaɓe na INEC.

Mata Sun Fi Maza Yawa a jadawalin Sabbin Masu Rajistar Katin Zaɓe na  INEC.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa jimillar mutane 3,867,997 ne suka kammala rajistar katin zaɓe a mataki na uku na shirin Ci Gaba da Rajistar Masu Zaɓe (CVR) domin shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.

Bisa ga bayanan hukumar, mata 2,037,589 ne suka yi rijista wanda ya kai kashi 52.68%, yayin da maza 1,830,408 suka yi rajista, wanda ya kai kashi 47.32%.

INEC ta bayyana cewa mutane 1,170,134 suka yi rajista ta yanar gizo, yayin da 2,697,863 suka kammala rajistarsu a cibiyoyin rajista da ke faɗin ƙasar.

Matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 ne suka fi yawa wajen yin rajista, inda suka kai 2,602,960, wato kashi 67.29% na dukkan sabbin masu rajista. 
Masu shekaru 35 zuwa 49 sun kai 843,757, yayin da masu shekaru 50 zuwa 69 suka kai 386,095. 
Masu shekaru 70 zuwa sama kuwa sun kai 35,185.

A bangaren sana'o'i, ɗalibai ne suka fi yawa da 892,946, sai masu kasuwanci da 810,452. Haka kuma manoma da masunta da matan gida da masu sana'ar hannu da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati da sauran jama'a sun yi rajista.

Hukumar ta kuma bayyana cewa mutane 41,092 ne masu nakasa suka kammala rajistar katin zaɓe, inda suka haɗa da makafi da kurame da zabiya da sauran nau'o'in nakasa.

A rabe-raben jihohi, Jihar Kano ce ta kasance kan gaba da 330,906 na sabbin masu rajista, sai Lagos, Delta da Edo da Ebonyi da Sokoto. A gefe guda kuma, Jihar Ekiti ce ta fi ƙarancin masu rajista, yayin da ba a gudanar da rajista a Jihar Osun ba saboda shirye-shiryen zaɓen gwamna mai zuwa.

INEC ta jaddada cewa adadin da aka fitar na wucin gadi ne, kuma za a tantance bayanan tare da amfani da tsarin tantance bayanan halittu (Automated Biometric Identification System) kafin a fitar da kundin masu zaɓe na ƙarshe.

0 Comment about the Post: