Monday, July 13, 2026

Iran Ta Ce Ta Kai Hari Da Jiragen Sama Marasa Matuƙa Kan Sansanonin Sojin Amurka dake ƙasar Kuwait.

A school headmaster in Oyo State has been kidnapped by suspected gunmen, who are demanding a ransom of ₦30 million for his release.

Rundunar Sojin Iran ta sanar cewa ta kaddamar da wani sabon hari ta amfani da jiragen sama marasa matuƙa kan sansanin sojojin Amurka ke amfani da su a Kuwait, tana mai cewa harin martani ne ga hare-haren da Amurka ta kai kan ƙasar Iran.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, ta ce an kai harin ne kan wuraren da ake zargin sojojin Amurka ke amfani da su, ciki har da tsarin kariyar sararin samaniya da cibiyoyin makamai masu linzami da mafaka da cibiyoyin tallafin kayan aiki.

Sojojin Iran sun ce wannan farmaki ya bambanta da hare-haren da Rundunar IRGC ta kai a wasu wurare da ke dauke da kadarorin sojin Amurka a yankin.

Iran ta zargi Amurka da kai hare-hare kan sansanonin sojinta da wasu muhimman ababen more rayuwa, tana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya.

Haka kuma ta yi ikirarin cewa hare-haren Amurka sun shafi hanyoyin sufuri da jiragen kamun kifi da jiragen dakon kaya da cibiyoyin hasashen yanayi, tare da zargin Amurka da katsalandan kan matakan tsaron Iran a mashigin ruwa na Hormuz.

Sanarwar ta kuma yi zargin cewa amfani da sansanonin soji da ke kasashen yankin Tekun Fasha da Amurka ke yi ya jawo wadannan kasashe cikin rikicin da ke tsakaninta da Iran.

Rundunar Sojin Iran ta jaddada cewa za ta ci gaba da kare ikon kasar da 'yancinta da cikakken ikon mallakar kasarta, tare da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da martani ga duk wani hari.

Sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin Amurka da na Kuwait ba su fitar da wata sanarwa da ta tabbatar ko ta musanta ikirarin da Iran ta yi ba.

0 Comment about the Post: