Saturday, July 4, 2026

Ƙasar Iran Ta Yabawa Kasashe Sama da 70 da Suka Halarci Jana'izar Ayatullah Ali Khamenei.

Ƙasar Iran Ta Yabawa Kasashe Sama da 70 da Suka Halarci Jana'izar Ayatullah Ali Khamenei.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yaba da halartar wakilai daga kasashe sama da 70 a jana'izar tsohon Jagoran Jamhuriyar Musulunci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, yana mai cewa hakan alama ce ta kyakkyawar dangantakar Iran da kasashen duniya.

A cikin sakon da ya wallafa a shafin X cikin harshen Larabci, Araghchi ya gode wa kasashen da suka aiko da wakilai domin halartar jana'izar, tare da yaba wa abin da ya kira "'yan'uwanmu Larabawa masu aminci" bisa goyon bayan da suka nuna.

An fara gudanar da jana'izar ne tun ranar Juma'a, kuma ana sa ran za ta ci gaba har zuwa ranar 9 ga watan Yuli. 
Wakilai daga kasashe da dama ciki har da Pakistan da Iraki da Saudiyya da China da Rasha sun halarta, tare da jami'an wasu kungiyoyin da ke kawance da Iran.

Mahukuntan Iran sun bayyana yawan mahalartan daga kasashen waje a matsayin shaidar irin tasirin diflomasiyyar kasar duk da rikice-rikicen da suka faru a yankin a 'yan watannin baya. 
Haka kuma, ana amfani da taron wajen tattaunawar diflomasiyya tsakanin jami'an kasashe kan batutuwan tsaron yanki da inganta dangantakar kasa da kasa.

Jana'izar na gudana ne bayan watanni na tashin hankali da rikicin da ya shafi Iran da Amurka da Isra'ila. 
Ana sa ran shugabannin Iran za su yi amfani da halartar wakilan kasashen duniya domin karfafa matsayinsu a tattaunawar diflomasiyya da ke gudana a matakin kasa da kasa.

0 Comment about the Post: