Gwamnatin Austria ta kaddamar da sabon ofishin 'yan sanda a gidan da aka haifi tsohon shugaban mulkin Nazi, Adolf Hitler, da nufin hana masu tsattauran ra'ayin Nazi mayar da wurin wajen ziyara da girmamawa.
Ginin, wanda ke garin Braunau am Inn kusa da iyakar Jamus, an bude shi a hukumance a ranar Laraba bayan an shafe shekaru ana shirye-shiryen gyaransa. Gwamnatin Austria ta sayi gidan a shekarar 2017, sannan ta sanar da shirin mayar da shi ofishin gwamnati a shekarar 2019. An kashe kusan Yuro miliyan 20 wajen gyaran ginin.
A wajen bikin bude ofishin, Magajin Garin Braunau, Johannes Waidbacher, ya ce wannan mataki yana nuna yadda garin ke fuskantar tarihinsa tare da daukar alhakin abin da ya faru a baya. Ministan Harkokin Cikin Gida na Austria, Gerhard Karner, shi ma ya halarci bikin tare da jami'an 'yan sanda da sauran manyan jami'an gwamnati.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Austria ta bayyana cewa mayar da gidan ofishin 'yan sanda zai rage darajarsa a idon masu tsattsauran ra'ayi tare da hana su amfani da shi a matsayin wurin taruwa ko ziyara.
Sai dai wasu masana tarihi da masu fafutukar yaki da wariyar launin fata sun ce sauya amfanin ginin ba zai goge tarihinsa ba. Robert Eiter na Kwamitin Mauthausen ya ce duniya ba za ta manta cewa a wannan gida aka haifi Adolf Hitler ba.
Wasu mazauna garin kuma sun bayyana rashin gamsuwarsu da sabon amfani da ginin, suna cewa sun fi son a mayar da shi cibiyar agaji ko wata cibiyar da za ta amfani al'umma.
Har yanzu akwai dutsen tunawa daga sansanin Mauthausen a gaban ginin, wanda aka rubuta a kansa kalmar "Kada a sake komawa mulkin kama karya." An kuma sanya sabon allo mai nuna cewa ginin yanzu ofishin 'yan sanda ne.
Matakin na daga cikin kokarin gwamnatin Austria na tinkarar tarihinta na mulkin Nazi tare da hana masu tsattsauran ra'ayi amfani da wurin wajen yada akidarsu.

0 Comment about the Post: