Kasar Amurka ta janye yawancin sojojinta da ta tura Najeriya na wucin gadi bayan kammala wani gagarumin aikin hadin gwiwa da rundunar sojin Najeriya ta gudanar kan mayakan kungiyar ISIS a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.
Kwamandan Rundunar Sojin Amurka ta Afrika (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson, ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai ta kafar intanet bayan taron shugabannin hafsoshin tsaro na kasashen Afrika na shekarar 2026 da aka gudanar a Luanda na ƙasar Angola.
A cewarsa, aikin ya mayar da hankali ne kan jagora na biyu na kungiyar ISIS a duniya, wanda ke kula da harkokin gudanarwa da yada farfaganda da daukar sabbin mambobi.
Ya bayyana cewa Amurka ta samar da bayanan sirri da wasu fasahohin soja na musamman, yayin da dakarun Najeriya suka jagoranci aikin a kasa.
Janar Anderson ya ce tura sojojin Amurka zuwa Najeriya na wucin gadi ne kawai, kuma mafi yawansu sun koma kasarsu bayan kammala aikin. Sai dai ya tabbatar da cewa kasashen biyu za su ci gaba da hadin gwiwa wajen musayar bayanan sirri da sauran dabarun yaki da ta'addanci.
Ya kara da cewa aikin ya raunana shugabancin kungiyar ISIS, ya katse hanyoyin sadarwarta, sannan ya haifar da karin mika wuya da ficewar wasu mayakanta a Arewa maso Gabashin Najeriya.
A nasa bangaren, Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya tabbatar da cewa sojojin Amurka da suka shiga aikin a watan Mayu sun zo ne domin wannan aiki kadai, kuma sun koma bayan kammala aikinsu.
Ya ce wannan runduna ta daban ce da wasu kusan sojojin Amurka 200 da ke Najeriya domin horaswa da bayar da tallafin fasaha.
Rahotanni sun nuna cewa hadin gwiwar ya kai ga kashe Abu Bilal Al-Minuki, mataimakin shugaban kungiyar ISIS, a maboyarsa da ke Jihar Borno.
Kasashen Najeriya da Amurka na ci gaba da karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro domin yaki da ta'addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Tafkin Chadi da Arewa maso Gabashin Najeriya.

0 Comment about the Post: