Rundunar 'Yan Sandan Jihar Nasarawa ta kama wani mutum mai suna Musbawu Amodu, mai shekara 30, bisa zargin dukan matarsa har ta rasu bayan wata takaddama da ta barke a gidansu da ke unguwar Angwan Yahaya, Agyaragu, a ƙaramar hukumar Obi.
Mai magana da yawun rundunar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne bayan an kai rahoto ofishin 'yan sanda na Agyaragu cewa ya yi wa matarsa mai shekara 20 duka, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta.
A cewar 'yan sanda, wanda ake zargin ya amsa cewa ya fusata ne bayan matarsa ta ƙi dafa masa abinci, abin da ya jawo gardama tsakanin su, wacce daga bisani ta rikide zuwa fada har ta rasa ranta.
Marigayiyar ta bar 'ya'ya biyu, namiji da mace, daga auren da suka shafe shekara shida suna yi.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, ya yi Allah wadai da wannan lamari, yana mai cewa tashin hankali a cikin gida abu ne mai muni da za a iya kauce masa. Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da bincike tare da gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

0 Comment about the Post: