Monday, July 6, 2026

An Bukaci Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross Ta Ziyarci Likitocin Falasdinu su Biyu Da Ke Tsare A gidan yarin Isra'ila.

An Bukaci Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross Ta Ziyarci Likitocin Falasdinu su Biyu Da Ke Tsare A gidan yarin Isra'ila.

Kungiyar Kare hakkin dan Adam ta Euro-Med ta yi kira ga Kungiyar Agaji ta duniya, Red Cross da ya gaggauta neman izinin ziyartar likitocin Falasdinu biyu, Dr. Hussam Abu Safiya da Dr. Marwan Al-Hams, da ke tsare a hannun Isra'ila, bayan rahotannin da suka nuna cewa suna fuskantar azabtarwa tare da tabarbarewar lafiyarsu.

A cewar kungiyar, Dr. Hussam Abu Safiya, daraktan Asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, na cikin mawuyacin hali. 
Lauyansa ya bayyana cewa bayan ziyararsa a ranar 2 ga Yuli, ya same shi da raunuka a sassa daban-daban na jikinsa, cikin matsananciyar kasala, tare da wahalar magana da numfashi.

Kungiyar ta kuma ce ta samu rahotanni masu sahihanci da ke nuna cewa Dr. Marwan Al-Hams, daraktan asibitocin wucin gadi na Gaza, na fuskantar cin zarafi yayin da yake tsare, lamarin da ya haddasa tabarbarewar lafiyarsa, ciki har da kamuwa da mummunar bugun zuciya.

Euro-Med ta bukaci a sako likitocin biyu cikin gaggawa, tana mai jaddada cewa su ma'aikatan lafiya ne fararen hula da dokokin jin kai na kasa da kasa ke ba kariya. 
Haka kuma ta nemi Red Cross ta samu damar ziyartar su domin tantance halin da suke ciki da kuma tabbatar da cewa sun samu kulawar lafiya cikin gaggawa.

Baya ga haka, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da hukumomin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya su gudanar da bincike kan zarge-zargen azabtarwa tare da daukar matakan da suka dace.

Sai dai kawo lokacin hada wannan rahoto, gwamnatin Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa kan sabbin zarge-zargen ba. 
A baya dai Isra'ila ta sha musanta zargin cin zarafin fursunoni, tana mai cewa ana tsare da su ne bisa tanade-tanaden dokokin kasar.

0 Comment about the Post: