Monday, June 29, 2026

Trump Ya Sanar da cewa Amurka da Iran a zasu tattauna a Qatar Duk da musayar Hare-hare a tsakaninsu

Trump Ya Sanar da cewa Amurka da Iran a zasu tattauna a Qatar Duk da musayar Hare-hare a tsakaninsu

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa za a gudanar da wata tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a Doha, babban birnin Qatar, ranar Talata, duk da ci gaba da samun rikicin soji tsakanin bangarorin biyu a yankin Tekun Fasha.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda ya ce Iran ce ta nemi a gudanar da ganawar. Sai dai har yanzu Iran ba ta tabbatar da cewa an shirya irin wannan tattaunawa ba.

“IRAN TA NEMI GANAWA. ZA A YI TA GOBE A DOHA!” inji Trump,  kamar yadda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.

Sanarwar Trump ta zo ne jim kadan bayan mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce ba a shirya gudanar da wata tattaunawa kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin Amurka da Iran a wannan makon ba.

Gharibabadi ya ce ana ci gaba da tuntubar Qatar, amma ya musanta rahotannin cewa ƙasashen za su yi taro a Doha.

Bambancin bayanan da suka fito daga Amurka da Iran ya haifar da rashin tabbas kan ko ganawar za ta gudana, ko da yake wasu jami'ai sun nuna yiwuwar a cimma matsaya daga baya.

Fadar White House ta ce wakilin musamman na Amurka, Steve Witkoff, da surukin Trump, Jared Kushner, sune za su jagoranci tawagar Amurka a tattaunawar da za a yi a Doha.

A baya-bayan nan Amurka da Iran sun cimma wata yarjejeniya da nufin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu, inda aka fara wani shirin tattaunawa na kwanaki 60 kan manyan batutuwa ciki har da shirin nukiliyar Iran.

Sai dai yarjejeniyar ta fuskanci kalubale sakamakon hare-haren da ake zargin Isra’ila na ci gaba da kaiwa a Lebanon da kuma takaddama kan mashigar ruwan Hormuz.

Iran ta yi watsi da duk wani tsari da zai rage mata iko kan mashigar ruwan Hormuz, yayin da hare-haren da Amurka ta kai kan wasu wuraren Iran suka biyo bayan martanin makamai masu linzami da jirage marasa matuka da Iran ta kai kan sansanonin Amurka a Bahrain da Kuwait.

Duk da wannan tashin hankali, ana ganin kokarin diflomasiyya na ci gaba.

Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce Amurka za ta ci gaba da bin yarjejeniyar da aka cimma, amma ta gargadi cewa duk wani hari kan muradun Amurka ko jiragen kasuwanci zai fuskanci martani.

Trump ya kuma bayyana cewa farashin man fetur ya fara sauka bayan yarjejeniyar, yana mai cewa kasuwannin mai sun samu sauki bayan Iran ta sassauta takunkumin da ya shafi mashigar ruwan Hormuz da kuma fitar da makamashinta.

0 Comment about the Post: