Aƙalla Falasɗinawa uku ne suka mutu, ciki har da wani yaro ɗan shekara takwas, bayan wani harin sama da Isra’ila ta kai a yankin Deir el-Balah da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda hukumomin lafiya suka bayyana.
Harin, wanda ya faru kusa da gadar Wadi Salqa a titin al-Baraka, ya kuma jikkata wasu mutane da dama. Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (Wafa) ya bayyana sunayen waɗanda suka mutu da Ali Fayez Isbaitan da Hassan Salman al-Hanajra, da Malik Wael Abu Shaweesh mai shekara takwas.
Wannan hari na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zargin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, inda hukumomin Falasɗinu ke cewa hare-haren Isra’ila na ci gaba duk da yarjejeniyar.
An kuma ruwaito cewa motocin sojin Isra’ila sun matsa zuwa titin Salah al-Din da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, tare da fuskantar rahotannin harbe-harbe da luguden wuta.
A arewacin Gaza kuma, an ce mutane biyu sun ji rauni sakamakon wani harin bam a Beit Lahiya.
Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza ya ce sama da Falasɗinawa 1,000 ne aka kashe, yayin da dubban wasu suka jikkata tun bayan fara yarjejeniyar tsagaita bude wutar.
Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta ce adadin mutanen da aka kashe a yaƙin da ya fara tun daga watan Oktoban 2023 ya ci gaba da ƙaruwa, inda dubban mutane suka mutu, wasu da dama kuma suka samu raunuka.
A halin yanzu, rahotanni sun ce sojojin Isra’ila na ci gaba da faɗaɗa yankunan da suke iko da su a Gaza tare da bayar da umarnin ƙaurar da wasu mazauna yankunan.

0 Comment about the Post: