Binciken hotunan tauraron dan adam da bidiyo da BBC News ta yi nazari a kansu ya nuna cewa hare-haren Iran sun lalata kusan sansanonin sojin Amurka 20 a fadin Gabas ta Tsakiya tun farkon rikicin da ya barke a waran Fabrairu, abin da ke nuna cewa barnar ta fi abin da aka riga aka bayyana yawa.
Rahoton ya bayyana cewa Iran ta kai hare-hare kan muhimman sansanonin soja a kasashe aƙalla takwas tun daga ƙarshen watan Fabrairu, ciki har da Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Qatar, Kuwait da Iraqi da Jordan da Bahrain da Oman.
An ce hare-haren sun lalata tsarin kariya ta sama da jiragen tankin mai na soja da na’urorin hango makamai, da sauran kayan aikin soja.
BBC Verify ta lura cewa barnar ta haɗa da manyan kayan aiki irin su tsarin kariya daga makamai masu linzami da jiragen leƙen asiri, inda aka kiyasta wasu daga cikinsu na da tsadar maye gurbi da ke kai miliyoyin daloli.
Rahoton ya kuma nuna cewa aƙalla jiragen sama 42, ciki har da na yaƙi da jiragen marasa matuƙa, na iya lalacewa ko kuma an lalata su a wannan lokacin.
Duk da cewa Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta ce ta riga ta kai hare-hare dubban wurare a Iran a yayin ayyukan da ake ci gaba da yi, jami’an Amurka sun ƙi yin tsokaci kan sabon binciken, suna mai cewa dalilai na tsaron aiki ne.
Masu sharhi da aka ambata a rahoton sun nuna cewa Iran ta sauya dabarunta a tsawon lokaci, daga amfani da manyan hare-haren makamai masu linzami zuwa kai hare-hare masu daidaito kan muhimman wuraren soja.
Sai dai wasu masana sun ce mai yiyuwa ne sojojin Amurka sun fara raina yadda hare-haren ke canzawa.
Wannan lamari na ci gaba da faruwa ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa duk wani sabon tashin hankali zai iya ƙara raunana tsarin kariyar sama da kuma shirye-shiryen soja a sansanonin Amurka da na ƙawayenta a yankin Gulf.

0 Comment about the Post: