Hukumar Tarihi ta Ƙasar Saudiyya ta sanar da gano wani rubutun dutse da ke ɗauke da sunan Halifa Umar ibn al-Khattab (RA) yayin binciken kayan tarihi a yankin Madina.
Hukumar ta bayyana wannan ganowar a matsayin wani muhimmin ci gaba a tarihin kayan gargajiya na addinin Musulunci na farkon zamani a ƙasar.
A cewar hukumar, rubutun yana daga cikin binciken kayan tarihi 1,774 da aka gano a mataki na farko da na biyu na wani babban bincike a gundumar Al-Mahd.
Kungiyoyin masu bincike sun kuma gano wurare 173 na tarihi da ba a taɓa sani ba a baya ba, abin da ke nuna irin dumbin tarihin da yankin ke da shi.
Daga cikin abubuwan da aka gano akwai zane-zanen dutse da ke ɗauke da sunan Umar ibn al-Khattab, wanda shi ne Halifa na biyu a tarihin Musulunci, tare da wasu tsofaffin waƙoƙin Larabci da aka sassaka a duwatsu.
Hukumar ta ce binciken ya kuma haɗa da zane-zanen dutse 1,259 da rubuce-rubucen Musulunci 461 da rubuce-rubucen Samudawa 34 da gine-ginen dutse 11 da fadoji uku da alamomin hanyoyin kasuwanci biyu da da rijiyoyi huɗu.
Umar ibn al-Khattab (RA), sahabin Annabi Muhammad (SAW), ya shugabanci al’ummar Musulmi daga shekara ta 634 zuwa 644 miladiyya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaɗuwar daular Musulunci ta farko.

0 Comment about the Post: