Friday, May 29, 2026

Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Jariri Da Wasu Mutane Biyu Daga Rijiyoyi A Kano

Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Jariri Da Wasu Mutane Biyu Daga Rijiyoyi A Kano

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ceto mutane uku, ciki har da wani jariri mai shekara daya da rabi, daga hatsarin fadawa rijiyoyi daban-daban a kananan hukumomin Kumbotso da Warawa na jihar.

Lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a tsakanin karfe 7:06 na safe zuwa 9:40 na safe, kamar yadda hukumar ta bayyana.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar, ya ce jami’an ceto sun fara samun kiran gaggawa daga yankin Semegu kusa da gidan burodin El-Sadeeq a Karamar Hukumar Kumbotso bayan wani mutum ya fada cikin rijiya.

Nan take aka tura jami’an ceto daga hedikwatar hukumar zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da wani mutum mai kimanin shekaru 40 a cikin rijiyar.

An ceto mutumin cikin halin suma sannan aka mika shi ga jami’an rundunar ‘yan sanda ta Panshekara domin ci gaba da bincike.

A wani lamari na daban da ya faru a kauyen Madarin Taba da ke Karamar Hukumar Warawa, jami’an kashe gobara sun kuma ceto wata mata mai shekaru 32 mai suna Maimuna Shitu tare da danta mai shekara daya da rabi, Harisu Muntari, bayan sun fada cikin wata rijiya.

Hukumar ta bayyana cewa ana zargin matar na fama da matsalar tabin hankali a lokacin da lamarin ya faru.

Jami’an ceto sun fito da matar da danta daga rijiyar cikin halin suma kafin a mika su ga shugabannin al’umma da iyalansu domin kula da lafiyarsu.

Hukumar ta ce har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin aukuwar wadannan lamura biyu.

Da yake martani kan lamarin, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya bukaci mazauna jihar da su tabbatar an rufe rijiyoyi yadda ya kamata domin kauce wa irin wadannan hadurra.

Ya kuma gargadi iyaye da masu kula da yara da su sanya ido sosai kan yara da kuma masu fama da matsalolin lafiya domin kare aukuwar makamantan hadurra.

Hatsarin fadawa rijiyoyi marasa kariya na ci gaba da zama babbar matsala a wasu yankunan Arewacin Najeriya, inda hakan ke haddasa raunuka da rasa rayuka a wasu lokuta.

0 Comment about the Post: