Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace fasinjoji ciki har da daliban da ke rubuta jarabawar JAMB, a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo na Jihar Benue.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Laraba, 15 ga Afrilu, lokacin da wata motar bas ta kamfanin Benue Links ke dauke da fasinjoji daga Makurdi zuwa Otukpo ta fuskanci harin 'yan ta'addan.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce motar na dauke da kimanin fasinjoji 18 lokacin da ‘yan bindigar suka tare ta kusa da Otukpo da misalin karfe 8 na dare, inda suka yi awon gaba da mafi yawan fasinjojin zuwa cikin daji.
Majiyar ta kara da cewa yawancin fasinjojin matasa ne maza da mata da ke kan hanyarsu ta zuwa Otukpo domin rubuta jarabawar JAMB da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis.
“Mutane biyu ne kawai—direba da wani fasinja—suka samu tserewa.
Yawancin fasinjojin matasa ne da suka yi tafiya domin rubuta jarabawar JAMB a yau,” in ji majiyar.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Ifeanyi Emenari, ya ce adadin wadanda aka sace ya kai 14.
Kwamishinan ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda ta fara bincike kan yadda lamarin ya faru, musamman dangane da tafiyar motar.
A cewarsa, kamfanin Benue Links yana da dokar hana zirga-zirgar dare, amma ana zargin direban ya dauki fasinjoji bayan lokacin aiki ya Kare ne.
“Amma yayin da muke bincike, muna bakin kokarinmu don tabbatar da an ceto wadanda aka sace,” in ji shi.

0 Comment about the Post: