Monday, April 20, 2026

“Netanyahu bai tilasta min shiga yaƙi da Iran ba,” in ji Donald Trump.

“Netanyahu bai tilasta min shiga yaƙi da Iran ba,” in ji Donald Trump.

Donald Trump ya bayyana cewa ƙasar Isra’ila ba ta tilasta masa shiga yaƙi da Iran ba, yana mai ƙaryata rahotannin da ke cewa shugabannin Isra’ila ne suka rinjaye shi ya ɗauki wannan mataki.

Trump ya ce shawarar shiga yaƙi da Iran shi ne ya ɗauka da kansa, ba tare da matsin lamba daga Isra’ila ba.
Ya jaddada cewa ya daɗe yana da ra’ayin cewa Iran bai kamata ta mallaki makaman nukiliya ba.
Ya kuma danganta matsayinsa da abubuwan tsaro da suka faru a baya, ciki har da hare-haren yankin Gabas ta Tsakiya. 
Rahotanni sun nuna cewa wasu sun yi zargin cewa firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya taka rawa wajen rinjayar Amurka shiga yaƙin.

Sai dai Trump ya fito fili yana cewa ba haka lamarin yake ba, yana mai kare kansa cewa manufofin ƙasarsa ne suka jagoranci matakin. 

Rikici tsakanin Amurka da Iran na ci gaba, tare da yunƙurin tattaunawa don kawo ƙarshen yaƙin.
Duk da haka, har yanzu akwai rashin tabbas kan ko tattaunawar za ta yi nasara. 

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: