Wata Babbar Kotun Tarayya ta umarci a saki Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Sunusi Khalifa Zaria da aka tsare bisa zargin hannu a shirin juyin mulki da ake zargin an yi niyyar yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kotu ta kuma ci tarar Hukumar Leken Asiri ta Soja (DIA) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) naira miliyan 2 kowanne, saboda keta hakkin dan adam na Malamin, musamman dangane da tsare shi ba bisa ka’ida ba da kuma rashin bin tsarin doka wajen gudanar da bincike.
Alkalin kotun ya bayyana cewa an tauye masa hakkin sa na kundin tsarin mulki, inda ya umarci a sake shi nan take ba tare da wani jinkiri ba.
Wannan hukunci na zuwa ne a cikin yanayin rikicin shari’a da bincike kan zargin shirin juyin mulki a Najeriya, wanda ya jawo kama mutane da dama tare da shiga kotu a lokuta daban-daban.

0 comments: