Iran ta sanar da sake rufe mashigar ruwan Hormuz, kwanaki kaɗan bayan ta bayyana cewa an buɗe ta, tana mai zargin Amurka da karya yarjejeniya ta hanyar ci gaba da kakaba takunkumin jiragen ruwa a yankin.
A cewar rundunar sojin Iran, an dawo da mashigar zuwa yanayinta na baya, inda yanzu take ƙarƙashin cikakken kulawa da ikon sojojin ƙasar. Hukumomin Iran sun bayyana matakin a matsayin martani ga abin da suka kira katsalandan da Amurka ke yi a harkokin zirga-zirgar jiragen ruwa.
Wannan mataki na zuwa ne bayan Iran ta amince a baya da buɗe mashigar domin jiragen kasuwanci su rika wucewa a takaice, amma ta ce matakin Amurka na ci gaba da takunkumi ya sa ta janye wannan sassauci.
Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai a duniya, inda kusan kashi 20% na man fetur na duniya ke wucewa ta cikinta, lamarin da ke sa duk wata tangarda a yankin ta shafi tattalin arzikin duniya.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ya ƙara tsananta a ‘yan kwanakin nan, musamman bayan kakaba takunkumin jiragen ruwa da kuma rikice-rikicen soja a yankin, lamarin da ke barazana ga tsaron sufuri da kasuwancin duniya.
Masana na gargadin cewa ci gaba da wannan rikici na iya haifar da ƙarin tashin farashin mai da kuma matsaloli a harkar samar da makamashi a duniya.

0 comments: