Saturday, April 18, 2026

Jagoran Addinin ƙasar Iran Ya Yabawa Sojojin ƙasar wajen Kare Ƙasar Daga Maƙiya.

Jagoran Addinin ƙasar Iran Ya Yaba wa Sojojin ƙasar wajen Kare Ƙasar Daga Maƙiya.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenie, ya yabawa sojojin ƙasar bisa jarumtaka da ƙwazon da suke nunawa wajen kare ƙasar daga hare-haren maƙiya, yayin wani saƙo da ya fitar domin bikin Ranar Sojoji ta ƙasa.

A cikin saƙon, jagoran ya jaddada cewa sojojin Iran sun taka muhimmiyar rawa wajen kare ‘yancin kai da cikakken ikon ƙasar, duk da barazanar da ke tattare da su daga waje.

Wannan yabo na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin tashin hankali a yankin, musamman bayan rikice-rikicen da suka shafi ƙasashen Amurka da Isra’ila.

Haka kuma, shugabannin rundunar sojojin sun jaddada cewa a shirye suke koyaushe domin fuskantar duk wata barazana, tare da nuna cewa suna da isassun kayan aiki da ƙwarewa na zamani domin kare ƙasar.

Ana gudanar da Ranar Sojoji a Iran duk shekara domin tunawa da sadaukarwa da nasarorin da sojojin ƙasar suka samu, tare da sake tabbatar da aniyar ƙasar na kare martaba da ikon ta.

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: