Tuesday, April 21, 2026

Donald Trump ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Iran.

Donald Trump ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Iran.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ƙasar Iran, domin bai wa tattaunawar zaman lafiya ƙarin lokaci, sai dai ya ce toshe hanyoyin ruwa na nan daram.

Trump ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa roƙon masu shiga tsakani daga Pakistan, yayin da ake jiran shugabannin Iran su gabatar da matsaya guda ɗaya kan yadda za a kawo ƙarshen rikicin. 

Sai dai duk da tsagaita bude wutar, ya jaddada cewa sojojin Amurka za su ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwa na Iran, tare da kasancewa cikin shiri idan tattaunawa ta gaza. 

Trump ya ce Amurka za ta dakatar da hare-hare na ɗan lokaci ne kawai, har sai an cimma matsaya a tattaunawar, ko kuma a yanke hukunci na ƙarshe. 

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu akwai rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu, musamman kan batun buɗe mashigar ruwan Hormuz, lamarin da ke da muhimmanci ga kasuwancin mai a duniya. 

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: