Thursday, April 23, 2026

An Kashe ‘Yar Jarida Amal Khalil a Harin Sama na Isra’ila a Kudancin Lebanon

An Kashe ‘Yar Jarida Amal Khalil a Harin Sama na Isra’ila a Kudancin Lebanon

Wata ‘yar jarida ‘yar ƙasar Lebanon mai suna Amal Khalil, ta rasu sakamakon harin sama da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon yayin da take aikin rahoton yaƙi a yankin, a cewar ma’aikaciyar kafar labarinta da jami’an ceto na yankin.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen al-Tiri, inda ta nemi mafaka yayin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Isra’ila da mayakan Hezbollah.

Rahotanni sun nuna cewa Amal Khalil tana aikin jarida ne a yankin lokacin da wani hari na farko ya tilasta mata da wani abokin aikinta neman mafaka a cikin wani gida da ke kusa.

Daga bisani, wani sabon harin sama ya auka kan wurin da suka fake, wanda ya yi sanadin mutuwarta.

Ma’aikatan ceto sun samu gawarta ne daga cikin baraguzan ginin bayan an samu jinkiri saboda ci gaba da hare-hare a yankin.

Amal Khalil ta yi aiki da jaridar Al-Akhbar ta Lebanon, kuma an santa da kawo Rahoto daga yankunan da ke fama da rikici a kudancin Lebanon da Bibiyar ayyukan sojojin Isra’ila a yankin.

Ta na da Kwarewa a aikin jarida na fagen fama tsawon shekaru

Kungiyoyin kare ‘yancin ‘yan jarida da hukumomin Lebanon sun yi Allah-wadai da kisan, inda suka yi kira da a kare ‘yan jarida da ke aiki a yankunan yaƙi.

Sojojin Isra’ila sun ce ba sa nufin kai hari ga ‘yan jarida kai tsaye, kuma sun ce suna binciken lamarin.

Wannan lamari na zuwa ne a lokacin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Isra’ila da Hezbollah, inda fararen hula da ‘yan jarida ke fuskantar haɗari yayin aikin rahoto.

Mutuwar Amal Khalil ta sake nuna irin haɗarin da ‘yan jarida ke fuskanta a yankunan yaƙi, tare da tayar da damuwa kan kariyar fararen hula da ‘yancin aikin jarida a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: