Sunday, April 26, 2026

An kashe Ministan Tsaron ƙasar Mali a wani hari da 'yan tawayen ƙasar suka kai gidansa.

An kashe Ministan Tsaron ƙasar Mali a wani hare-hare da 'yan bindiga suka kai gidansa.

Rahotanni daga Ƙasar Mali sun tabbatar da cewa Ministan Tsaron ƙasar, Sadio Camara, ya rasu bayan wani harin haɗin gwiwa da 'yan tawayen ƙasar suka kai masa a garin Kati, kusa da babban birnin ƙasar Bamako.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan tawayen sun kai hari gidan ministan ne a lokacin da suke ci gaba da kai jerin hare-haren haɗin gwiwa a sassa daban-daban na ƙasar. 
Garin Kati, wanda yake da muhimmanci ga rundunar soji, ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da aka fi kai harin.

Ana zargin cewa mayakan da ke da alaƙa da ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wacce ke da nasaba da al-Qaeda, ne suka jagoranci hare-haren tare da wasu ‘yan tawaye na Tuareg.

Hare-haren sun shafi wurare da dama a Mali, ciki har da:

Bamako

Kati

Gao

Kidal

Mopti

Rahotanni sun baiyana cewa an yi amfani da manyan makamai masu fashewa, lamarin da ya sa harin ya zama ɗaya daga cikin mafi muni a ‘yan shekarun nan.

An bayar da rahotan cewa har yanzu ana jin karar bindiga a wasu wurare, yayin da sojojin Mali ke kokarin daidaita al’amura. 
,Har yanzu ba a tabbatar da cikakken bayani kan yawan asarar rayuka ba.

Mutuwar Sadio Camara na iya zama babbar illa ga gwamnatin sojin Mali, domin yana daga cikin manyan jagororin mulkin ƙasar.

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: