Hakika zamani yazo inda 'yan farfagandan Addini da Jahilai ke cin karansu babu babba ka.
Inda zaka ga mai da'war malanta ya saki koyarwar ANNABI ﷺ ya bi son ranshi ko na wani malamin da ya yarda da shi.
Don haka Al'ummar musulmi sun shiga wani yanayi na tashin hankali Wanda ire-iren wadancan malaman masu da'awar Sunnah suka yi sular kasancewar mu a ciki, ta hanyar dagewa akan sai Musulmi ya yarda da Hadisai wadanda suke taba Janibin ANNABI ﷺ.
Sun manta cewa ba kowane Hadisi bane zai iya zama gaskiya musamman Wanda ya ci karo da ayoyin Alkur'ani Mai girma.
Zamu fahimci cewa hatta magabata sun yi iya kokarinsu wajen Kiyaye ruwaito hadisan da basu da tabbaci akansu ko Kuma suka ci karo da ka'idoji ingancin Hadisi.
Misali:
Imam Malik, cikin hadisai dubu dari ya dinga tacewa har muwaɗɗa ta dawo hadisai dubu ɗaya.
Ahmad Dan Hanbali cikin hadisai miliyan daya ya zubda dubu dari tara da wani abu ya rubuta dubu talatin da wani abu a Musnad.
Bukhari ya tace Hadisan littafensa ne daga hadisai miliyan guda, sannan ya tace sama da dubu dari dara tara, sannan ya rubuta dubu biyu da wani abu yayi (2,800) sannan yayi watsi da sama da hadisi dubu biyu wanda Muslim ya yarda da ingancinsu har ya saka su cikin littafensa na sahihi.
Shi kuma Muslim yabar hadisai fiye da dari tara wanda Abokinsa Bukhari yayi imani da su, bai ruwaice su ba saboda a wurinsa basu inganta ba.
Ƙarshe Albani yazo yayi Silsilatul Ahaadisis swahiha ya kawo Hadisan da ya yi imani da su ne sahihai, sannan yayi Silsilatul Ahaadisis Da'iyfah anan ma ya mangare sama da hadisai dubu goma.
Kowa da Hadisan da ya kwasa dai dai da abin da ya gamsu da shi, a wurinka zaiyu maganar Annabi ce, a wurin wancan cikakkiyar qarya ce, a wurin wancan cikakkiyar qarya ce, a wurinka a maganar Annabi ce, shi yasa ake cewa suna faidantar da zato ne ba yaqini ba.
Allah madaukakin sarki ya bamu ikon gane gaskiya da Kuma bin ta komai dacinta.

0 comments: