Wajibin kowane musulmi ne ya kiyaye taba Janibin ANNABI MUHAMMAD ﷺ ko jingina maShi wani tawaya, matukar mutum yana son ya tsira da imaninsa.
Ina wannan maganar ne ga masu mummunar kalmar batanci ga iyayen ANNABI MUHAMMAD Sallallahu Alaihiwasallam, wadanda suka jahilci addini Kuma suke kokarin kawo fitina acikinsa.
"Hakika Babu wani hadisi wanda annabi ﷺ ya fito ƙarara ya bayyana sunan mahaifin da ya haifeshi Sayyadina Abdullahi (A.S) yace yana wuta, ba wannan hadisin.
Haka zalika Babu wani hadisi ƙarara, wanda Manzon Allah ﷺ ya fito ya bayyana sunan mahaifiyarsa Nana Aminatu (A.S) da ta haifeshi yace tana wuta, babu wannan hadisin, duk abin da wani zai kafa maka hujja dashi, to abu ne wanda yana iya ɗaukar ma'ana kaza, sannan yana iya ɗaukar ma'ana kaza"
Kuma "Kuskure ne babba kanka tsaye kace iyayen annabi Muhammadu (S.A.W) kace suna cikin wuta haliyyan, domin haƙiƙa babu ladabi a cikin hakan, sabida ko kai baza kaso kaji ance iyayenka ƴan wuta ba ne ko da kuwa sun mutu a cikin shirka ne"
"Ko da iyayen annabin ba a musulunci suka rasu ba, to haƙiƙa rashin ladabi ne kanka tsaye kace su ɗin ƴan wuta ne, kuma ka auna da naka iyayen tukunna, tabbas za kaji zafin hakan".
