A cikin wannan bidiyon Sheikh muhammad Auwal yayi bayani ne game da ayar Alkur'ani dake cewa "Idan kuka juya baya Allah madaukakin sarki zai canja ku da wasu mutane Wanda baku ba, sannan ba zasu zamo lalatattu irinku ba".
inda ya kawo tafsirin ayar daga cikin Tafsirin na littafin Mafatih al-Ghaib (Tafsir Al Kabir) na Sheikh Fakhr al-Din al-Razi.
Yayi bayanin ne game da yakin dake faruwa a tsakanin jumhuriyar musulunci ta Iran da haramtacciyar kasar Israi'la yayin da Kasashen larabawa wadanda aka saukar da musulunci da harshensu ke cigaba da kawance da hulda na biliyoyin daloli da Amurka wacce babbar abokiya ko kuma mu ce uwar gijiyar israi'la.
Latsa wannan bidiyon dake kasa domin sauraron cikakken jawabin.
0 comments: