Hakika kyautatawa mutane abu ne dake kusantar da bawa zuwa ga Allah da samun mafificin sakamakon shiga Aljanna kamar yadda yazo a cikin hadisan manzon Allah (S.A.W).
Daga abi Hurairata R.A yana cewa:
'Lallai wani Mutum yace; ya Manzon Allah,Lallai wance, sai ya bada labarin yawan sallarta ta nafila da yawan azuminta na nafila, sai tana cutar da Makwabtanta da harshenta sai Annabi s.a.w yace:
"Tana wuta"(wato yar wutace). Sai ya sake baima Annabi s.a.w Labarin wata mata,da karancin Ibadarta, karancin sallarta ta nafila, da karancen azumin na nafila,kuma bata yin sadaqa daga dukiyarta ko kadan,sai dai bata cutar da makwabtanta". Sai Annabi s.a.w yace yar aljannace.
#Riyaduss Saleehina.
Kada yawan ibada ya rudeka ka rika cutar da mutane sai yin hakan yasanya kayi asarar lahirarka. Annabi s.a.w yana cewa duk wanda yayi Imani da Allah da ranar Lahira,to ya girmama makwabcinsa. Riyaduss Saliheena.
Annabi s.a.w yana cewa Mala'ika Jibrilu bai gusheba yana yimin wasiyya akan makwabciba, har sai danayi tsammanin idan makwabci zaiyi gadon makwabci.
#Saheehul Jami'I.
Yana cikin cutar da makwabci:
-Wulakantaci ko cin mutuncinsa agabansa ko bayan idansa.
-Yin zina da diyarsa ko matarsa ko kanwarsa.
-chanza alamar gona ko fege ko gida. Ta hanya shiga wani kasonsa ba tare da izininsaba.
-Rashin kulawa da duk wani abu da zai cutar dashi kamar Bola ko kwata ko warin bandaki ko ka tada inji da zai hanashi barci.
-kawo wani abu anguwa da zai lalata tarbiyar yaransa dana sauran yan unguwa.
-idan mai karamin karfina kaki taimakonsa cikin abinda babu ikon.
Da dai sauransu.
ANNABI S.A.W yana cewa;
"Wallahi baiyi imani ba, wallahi baiyyi imaniba, sai Sahabbai,sukace wanene wannan ya rasulullah?, sai ANNABI S.A.W yace wanda Makwabcinsa bai kubuta daga sharrinsa ba".
#Riyaduss Saliheena.
Hakika matsayin makwabci abune mai girma a cikin koyarwa ta musulimci.
Malamai suna kasa makwabci zuwa gida ukku.
1-Makwabci mai hakki guda uku, wato makwabcinka sannan musulmine sannan dan uwankane na jini. Wannan shine wanda hakkin makwabtaka yafi girma fiye da sauran kowane makwabci wanda bashiba.
2-Makwabici Musulmi, wannan yana da matsayin hakki guda biyu ga hakkin makwabtaka ga hakkin musulinci.
3-Makwabci wanda. Ba musulmi ba, wannan yana da hakki guda daya kadai wato hakkin makwabtaka.
Sannan suna kasa makwabtaka kashi biyu.
1- akwai makwabci babba, shine makwabcin da rayuwr hadaku ga gidanka ga nasa,ko gona ta hadaku ma'ana zaku tsawon lokaci kuna tare.
2- akwai makwabci na wucin gadi,shine wanda wani abu mai karamin lokaci ya hadaku kamar hawa mota ko jirgi ko class da dai sauransu.
Allah ka bamu ikon kyautatama makwabtanmu aminn.
0 comments: