Tuesday, May 6, 2025

Farillan sallah da sunnonin sallah

Farillan sallah da sunnonin sallah

A cikin wannan mukalar zamu kawo maku farillan sallah da sunnonin sallah domin amfanuwar Al'ummar Musulmi wadanda ke Neman sani.

BABIN FARILLAN SALLAH:
Farillan sallah guda goma sha biyar 15 ne Kuma wajibin kowane Musulmi ne ya San mu domin yin Sallah bisa koyarwar shari'ar Musulunci.

Farillan Sallah Sun Kasu Ne Gida 2:
 1. Sharuddan Sallah
 2. Rukunan Sallah 
Kuma akwai bambanci tsakanin Sharadi da kuma Rukuni. Sharadi ana samunsane kafin a shiga cikin ibada, shi kuma Rukuni ana samunsane a cikin ibadar, kuma dole sai kowanne yasamu sannan ibada take cika.

 SHARUDDAN SALLAH:-
1. Muslunci 
2. Hankali 
3. Balaga 
4. Tsarkin kari 
5. Tsarkin dauda 
6. Shigowar lokacin sallah 
7. Suturce al-aura 
8. Fuskantar alqibla. 

Kuma gabadayan Malamai sun yi IJAMA’I akansu, sai dai Malamai sun yi sabani akan cewa shin NIYYA da KABBARAR-HARAMA su ma sharadi ne ko kuma ba SHARADI ba ne?

RUKUNAN SALLAH:-
1.Tsayuwa  
2.Ruku’i  
3.Sujjada  
4.Zaman karshe.

Wannan ma gabadayan Malamai sun yi IJMA’I akansu, saidai Mazhabin SHAFI’IYYA sun kara da wadansu abubuwa kamar haka:-
1.Daidaituwa acikin Ruku’i  
2.Zaman da’akeyi tsakanin sujjada guda biyu  
3.Tahiyar karshe  
4.Salati ga Annabi(ﷺ) 
5. Sallama. 

FARILLAN SALLAH:
1-SHIGAR LOKACI:-salla bata yiyuwa sailokacinta ya shiga.

2-TSARKI:- Wajibine mai salla ya zamto yana da tsarki tundaga ta da ikama zuwa lokacin da zai idarda salla.

3:-NIYYA:- Itace kudurcewar niyyar salla dazakayi ko azaharce ko la'asar da sauransu.

4-KABBARAR HARAMA:-Itace kabbarar farko dazaka bude salla da ita.

5-TSAYUWA DOMIN KABBARAR HARAMA:-Wajibin ­e kakasance kana tsaye lokacinda kake kabbarar haramar shiga salla.

6-KARATUN FATIHA. karanta suratul fatihah wajibi ga Mai yin Sallah.

7-TSAYUWA DOMIN KARATUN FATIHA.

8-YIN RUKU'U.

9-DAGOWA DAGA RUKU'U.

10-YIN SUJJADA.

11-DAGOWA DAGA SUJJADA.

12-ZAMA NA BIYU:-Zaman karshe wanda za’ayi sallama acikinsa  

13-DAIDAITUWA:- ­Kakasance ka daidaitu atsaye. baka waiwaye ko kalle-kalle, haka kuma idan a zaune kake, ko yayin ruku'u da sauran abubuwan da ke faruwa a lokacin yin sallah.

14:-NATSUWA:- ­wajibine mai yin sallah ya samu natsuwa yayin gabatar da ita, ka sani cewa kana gaban ubangijinka mai tsarki ne, Kaji tsaronsa acikin zuciyarka, kabautamasa da natsuwa, Bakamagana ko kalle-kalle yayin sallah.

15-SALLAMA:- Itace sallamar fita daga sallah.

Article Translation in English Language.

In this article we will bring to you the obligatory parts of the prayer and the sunnah parts for the benefit of the Muslim community who seek to know. 

Chapter on the Precepts of Prayer: There are fifteen obligatory parts of the prayer and it is the duty of every Muslim to know each part in other to pray according to the teachings of Islamic law. 

The obligatory parts of prayer are divided into 2: categories: 
1. Conditions of Prayer 
2. Principles of Prayer.
And there is a difference between Condition and Principles. Conditions are met before engaging in worship, and Principles are met during worship, and must be met by everyone before worship is completed.

SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: