Sallama itace farkon abinda Allah yayi Umarnin Annabi Adamu ﷺ ya aikata,sannan itace farkon alaqa tsakaninsa da Mala'ikun Allah.
Sallama itace gaisuwar Allah zuwa ga bayinsa zababbu, kuma itace gaisuwar 'yan aljanna a tsakaninsu. Assalamu Alaikum amincin Allah ya tabbata a gare Ka.
Farkon Sallama aminci ne tsakiyarta albarka ne, sannan karshenta soyayya ne tsakanin juna.
Sallama tana sanya kauna da soyayya tsakanin juna,soyayya a tsakanin juna tana tabbatar da Imani, imani kuma shine kadai yake kai mutum zuwa aljanna.
Sallahma itace babbar alamar aminci tsakanin juna,kuma itace babban abinda yake hada kai tsakanin musulmi da musulmi,wanda yayi ta ya nuna aminci wanda akayiwa ya sami aminci.
Yin Sallama Mustahabbine amma amsata wajibine, idan baka amsa sallama ba to wanda yafika alkhairi shine zai amsa, domin ita sallama bata tafiya a banza.
Yada sallama tsakanin musulmi wanda kasani da wanda bakasani ba cikasa umarnine na Manzon Allah ﷺ.
Karami shi yake fara yiwa babba sallama, kamar mutane 'yan kadan su zasu fara yiwa masu yawa sallama, haka kuma mai tafiya shine zai fara yiwa na kasa sallama, na kan abin hawa shi zai fara yiwa mai tafiya akasa sallama.
Manzon Allah ﷺ yana yiwa yara sallama,sannan yana yiwa mata sallama,kaima zaka iya yiwa mata sallama idan baka tsoron fitina.
Sallamata tana farawa da lada goma tana karewa da lada talatin.
Assalamu alaikum
*Lada goma*
Assalamu alaikumu warahmatullah
*Lada Ashirin*
Assalamu alaikumu Warahmatullahi Wa barakatuhu
*Lada talatin*.
Amsa sallamama haka yake wajan samun lada,daga goma zuwa Talatin, iya lafazinka iya ladarka.
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
"Ina rantsuwa da Wanda raina ke hannunshi! Ba zaku shiga Aljanna ba har sai kunyi Imani, Kuma ba zaku yi Imani ba har sai kun so junanku. Shin in Baku labarin Wani Al'amari wanda idan kuka aikata shi zaku so junanku? Ku yada sallama a tsakanin juna". (Sahih Muslim).
Abinda Manzon Allah ﷺ yake nufi shine:
Mu bayyana sallama a tskanin junanmu saboda sanadiyyar yada sallama da bayyanata a tsakaninmu zamu sami soyayya da kaunar junanmu wanda hakan shine cikar imani.
Allah ne mafi sani
Assalamu Alaikumu Warahmatullahi Wa barakatuhu.
Article Translation in English Language.
Sallama is the first thing that God commanded Prophet Adam ﷺ to do, then it is the first relationship between him and the Angels of God. Salam is the greeting of God to His chosen servants, and it is the greeting of the people of Paradise among them.
Assalamu Alaikum, may God's peace be upon you. The beginning of Peace is loyalty, the middle is blessing, and the end is love between each other.
Peace makes love and affection between each other, love between each other confirms faith, and faith is the only thing that takes a person to paradise.
Sallama is a great sign of mutual trust, and it is the main thing that unites Muslims and Muslims, the one who does it shows loyalty and the one who does it gets loyalty.
Saying Sallama first is Mustahabbin but answering is obligatory, if you don't answer salam, then the one who does good will answer, because salam does not go in vain.
Spreading greetings among Muslims to someone you know and someone you don't know is a fulfilling the command of the Messenger of God ﷺ.
The younger one is the one who greets the older one first, just like few people will greet the many people first, and the pedestrian will greet the lower one first.
The Messenger of God ﷺ greets the children, then greets the women, you can greet the women if you are not afraid of the trial.
Sallamata begins with ten rewards and ends with thirty rewards.
Peace be upon you
*ten rewards*
Assalamu alaikum warahmatullah *Twenty Rewards* Assalamu
Alaikum Warahmatullahi Wa Barakatuhu
*Thirty rewards*.
The answer to salam is the same when you get a reward, from ten to thirty, you can pronounce it, you can get your reward. The Messenger of God ﷺ says:
"I swear by the One in whose hands my soul is! You will not enter Paradise until you believe, and you will not believe until you love each other. Shall I tell you about a matter that if you do it, you will love each other? Spread greetings among each other". (Sahih Muslim).
What the Prophet ﷺ means is:
To Spread greeting to each other because due to the spread of greeting and saying it among us, we will have love and affection for each other which is the fulfillment of faith.
0 comments: