Ƙasar Iran ta fara shirye-shiryen gudanar da makon jana'iza da zaman makoki na Jagoran Addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu sakamakon hare-haren sama da Amurka da Isra'ila suka kai yayin rikicin baya-bayan nan a watan Fabrairu.
Za a fara gudanar da jana'izar a birnin Tehran, kafin a ci gaba da bukukuwa da zaman makoki a biranen Qom da Mashhad. Haka kuma, za a gudanar da wasu bukukuwa na musamman a biranen Najaf da Karbala na kasar Iraki.
Mahukuntan Iran sun shirya motocin sufuri da rangwamen masauki a otal-otal da wuraren kwana a makarantu da masallatai da dakunan wasanni domin saukaka wa miliyoyin masu makoki da ake sa ran za su halarci jana'izar.
Jami'an gwamnati sun bayyana cewa yawan mahalarta jana'izar zai nuna ci gaba da goyon bayan al'ummar kasar ga Jamhuriyar Musulunci duk da kalubalen da kasar ta fuskanta bayan yakin.
Mutuwar Ayatollah Ali Khamenei na daga cikin manyan abubuwan da suka faru a tarihin Iran na zamani. Bayan rasuwarsa, dansa Mojtaba Khamenei ya karbi jagorancin kasar a matsayin sabon Jagoran Koli, bayan shi ma ya samu munanan raunuka a harin da ya kashe mahaifinsa.
An tsaurara matakan tsaro a fadin kasar, inda aka takaita zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Tehran da sauran manyan birane. Haka kuma, gwamnatin Iran ta gargadi Amurka da Isra'ila kan yiwuwar mayar da martani mai tsauri idan aka sake kai wani hari yayin gudanar da jana'izar.
Duk da cewa gwamnati na sa ran miliyoyin mutane za su halarci jana'izar, masu nazarin siyasa sun ce ra'ayoyin al'ummar Iran sun kasu. Wasu 'yan kasar na ci gaba da nuna damuwa kan matsin tattalin arziki da takunkuman kasa da kasa da kuma yanayin siyasar cikin gida, lamarin da ya sa wasu suka zabi barin Tehran maimakon halartar bukukuwan jana'izar.
Ana sa ran manyan baki daga kasashe ciki har da Rasha da China za su halarci bukukuwan bankwana, yayin da za a binne Ayatollah Ali Khamenei a birnin Mashhad bayan kammala makon jana'izar.

0 Comment about the Post: