Mataimakin Shugaban Ƙasar Amurka, JD Vance, ya isa Switzerland domin tattaunawa da jami’an Iran kan yadda za a ƙarfafa yarjejeniyar wucin gadi da nufin kawo ƙarshen rikicin Amurka da Iran.
Ana gudanar da tattaunawar ne a wurin shakatawa na tsaunin Buergenstock da ke Switzerland, inda ake sa ran bangarorin biyu za su tattauna batutuwan tsagaita bude wuta na dindindin da shirin nukiliyar Iran da kuma halin da ake ciki a Lebanon.
Tawagar Amurka na ƙarƙashin jagorancin Vance, yayin da tawagar Iran ke ƙarƙashin jagorancin babban mai shiga tsakani, Mohammad Bagher Ghalibaf. Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ma yana cikin tawagar Iran.
Kafin ya tashi zuwa Switzerland, Vance ya bayyana cewa tattaunawar za ta mayar da hankali kan samun ci gaba kan batun nukiliya da kuma tsagaita bude wuta a Lebanon, yana mai cewa ana iya ɗaukar kwanaki kafin a kammala.
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, da shugaban rundunar sojin ƙasar, Asim Munir, su ma sun isa Switzerland domin shiga tsakani a tattaunawar.
Wannan taro ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tashin hankali bayan Iran ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta hanyar kai hare-hare a Lebanon.
Rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da rufe mashigar ruwan Hormuz a matsayin martani, amma sojojin Amurka sun ce jiragen kasuwanci suna ci gaba da wucewa.
Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur da iskar gas a duniya. Rundunar Tsaron Amurka ta ce jiragen ruwa da dama sun wuce ta mashigar tare da ɗauke da miliyoyin ganga na mai.
Iran ta bukaci a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar, ciki har da dakatar da yaƙi a Lebanon da sake buɗe mashigar ruwan Hormuz da sakin kadarorin Iran da aka kulle, da kuma cire takunkumin Amurka kan ɓangaren makamashin ƙasar.
Halin da ake ciki a Lebanon na ci gaba da zama mai rauni, inda Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah ke zargin juna da karya yarjejeniyar.
Isra’ila ta ce tana mayar da martani ne kan hare-hare, yayin da Hezbollah ta ce Isra’ila ce ta fara karya yarjejeniyar.
Ana sa ran tattaunawar Switzerland za ta nuna ko yarjejeniyar wucin gadi za ta iya kaiwa ga samun cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya.

0 Comment about the Post: