Sunday, April 19, 2026

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Sarki a Jihar Kwara, Sun Yi Garkuwa da Sarki da Matarsa.

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Sarki a Jihar Kwara, Sun Yi Garkuwa da Sarki da Matarsa.

A jihar Kwara, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki a fadar wani sarki da ke yankin Olayinka a ƙaramar hukumar Ifelodun, inda suka yi garkuwa da sarkin yankin da matarsa, da wani mutum guda.

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne da daddare, inda maharan suka kutsa cikin fadar suna harbi domin tsoratar da jama’a kafin su tafi da mutanen da suka kama. Lamarin ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin.

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun zo da makamai masu yawa, kuma babu wanda ya iya tunkaransu saboda tsananin tsoro da suka haifar a yankin.

Har zuwa yanzu, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani ba, amma ana ci gaba da kokarin gano inda aka kai waɗanda aka yi garkuwa da su.

Mazauna yankin sun bayyana damuwa kan yadda matsalar garkuwa da mutane ke ƙaruwa a jihar, tare da kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: