Wani fitaccen dan siyasa kuma ɗan kasuwa, Ambasada Abubakar Sadeeq Plaza, ya bai wa wata ƙaramar ‘yar kasuwa, Misis Sarah Luka, kyautar Naira 500,000 bayan ta mayar da Naira miliyan 1 da ta tsinta a ɓoye cikin kayayyakin da ta saya a kasuwar Terminus da ke Jos.
Rahotanni sun nuna cewa Misis Luka ta gano kudin ne bayan ta sayi wasu kaya a kasuwar, inda daga bisani ta yanke shawarar mayar da su ga mai su ba tare da ɓata lokaci ba. Wannan hali nata na gaskiya da riƙon amana ne ya jawo yabon jama’a da kuma wannan kyauta daga Ambasada Sadeeq Plaza.
Al’ummar yankin sun jinjinawa wannan kyakkyawan aiki, suna mai cewa hakan abin koyi ne ga sauran mutane wajen nuna gaskiya da amana a cikin harkokin yau da kullum.

0 comments: