Rundunar sojin Isra’ila ta amince da sake mayar da wasu sojojin ƙasar bakin aiki, duk da cewa ana zargin su da cin zarafi da lalata ga wani Bafalasɗinue da ke tsare a hannunsu.
Rahotanni sun bayyana cewa babban hafsan sojin Isra’ila ya amince da wannan mataki ne bayan shari’ar da ta shafe lokaci mai tsayo tana gudana kan zargin da aka yi wa sojojin a sansanin tsare fursunoni na Sde Teiman.
A baya an gurfanar da sojojin ne bisa zargin azabtarwa da kuma cin zarafin wani fursuna na Falasɗinu, wanda ya jawo cece-kuce da zanga-zanga a cikin Isra’ila da ma kasashen waje.
Sai dai daga bisani, rundunar sojin ta ce ta dakatar da tuhumar tare da dawo da sojojin bakin aiki, matakin da ya jawo suka daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama, wadanda ke ganin hakan na nuna rashin hukunta masu laifi.
Lamarin ya ci gaba da tayar da muhawara kan yadda ake kula da fursunonin Falasɗinu a lokacin rikicin Gaza.
0 Comment about the Post: