JAMB ta sauya lokacin fara jarabawar UTME a Jos saboda matsalar tsaro.

JAMB ta sauya lokacin fara jarabawar UTME a Jos saboda matsalar tsaro.

Hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a, JAMB ta sanar da sauya lokacin fara jarabawar UTME a birnin Jos, sakamakon matsalolin tsaro da ke faruwa a yankin.

A cewar rahoton, Hukumar ta JAMB ta bayyana cewa jarabawar da aka tsara gudanarwa daga 16 zuwa 25 ga Afrilu za ta fara ne da ƙarfe 9:00 na safe maimakon 8:30 na safe a cibiyoyin jarabawa da ke Jos.

Matakin na zuwa ne domin tabbatar da tsaron ɗalibai da kuma sauƙaƙa musu samun damar isa cibiyoyin shirya jarabawar ta CBT lafiya, musamman a wuraren da ake fama da tashin hankali.

Rahotanni sun nuna cewa wasu dalibai da iyaye sun nuna damuwa kan yadda za su rika tafiye-tafiye zuwa cibiyoyin jarabawa a wasu sassan birnin saboda matsalar tsaro.

Duk da wannan sauyi, hukumar ta JAMB ba ta sauya ainihin jadawalin jarabawar UTME ba, domin jarabawar za ta ci gaba kamar yadda aka tsara a faɗin ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form