Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasar Iran ba ta neman yaki kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da ƙasashen duniya.
Sai dai ya jaddada cewa duk wani yunkuri na abokan gaba na tilasta wa Iran abin da ba ta yarda da shi ba, ko kuma ƙoƙarin tilasta mata ta mika wuya, “zai ci tura.”
Pezeshkian ya ce Iran na ci gaba da fifita hanyoyin diflomasiyya wajen warware rikice-rikice, amma za ta tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancinta da muradunta idan aka matsa mata ko aka yi mata barazana.
Ya ƙara da cewa Iran ba za ta taɓa mika kai ga matsin lamba ba, duk da cewa ƙofa ta tattaunawa da fahimtar juna har yanzu a buɗe take.
Tags
Labaran Duniya
