IAEA ta yi gargadi kan karuwar ayyukan nukiliya a ƙasar Koriya ta Arewa.

IAEA ta yi gargadi kan karuwar ayyukan nukiliya a ƙasar Koriya ta Arewa.

Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya bayyana cewa an samu “gagarumin ƙaruwa cikin sauri” na ayyuka a tashar nukiliya ta Yongbyon da ke ƙasar
 Koriya ta Arewa.

Ya ce wannan ci gaban na nuna “tsananin ƙaruwa mai haɗari” a ƙarfin Koriya ta Arewa na samar da makaman nukiliya, inda ake kiyasin cewa ƙasar na iya mallakan makaman nukiliya mai tarin yawa.

Hukumar ta ce wannan lamari na bukatar kulawa mai tsanani daga kasashen duniya, saboda yana iya ƙara tayar da hankalin tsaro a duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form