Wednesday, October 29, 2025

Abubuwan al'ajabi dake tattare a halittar Rakumi

 Abubuwan al'ajabi dake tattare a halittar Rakumi


Shin ka taɓa karanta aya ta (17) cikin suratul Gashiya inda Allah madaukakin sarki yake cewa: 

﴿أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ﴾
[ الغاشية: 17]

"Shin basu duban raƙumi 🐫 yadda aka halitta shi"

Muje zuwa binciken masana domin sanin sirrin dake tare dashi👇

Wani abun burgewa dangane da halittar raƙumi 🐫 da Ubangiji Madaukakin Sarki yayi;

Raƙumi 🐫 yana iya shan ruwan teku mai gishiri da kuma ruwan kogi ko kuma ruwa maras gishiri: Ubangiji ya halitta ƙoda (kidney) na raƙumi 🐫 yadda zai iya tace gishiri mai yawa daga ruwan teku, yadda zai zamto daidai domin amfani a jikinsa, sauran gishiri kuma zai zamto ya fita ne ta hanyar fitsari 

Raƙumi 🐫 yana iya cin ƙaya ba tare da ta cutar dashi ba dalili: yawun raƙumi 🐫 yana da kauri, hakan yana bashi daman sanya ƙaya tayi laushi ba tare da ta cutar dashi ba.

Leɓɓan shi da kuma da kuma cikin bakin shi suna da tauri sosai, hakan yasa yake iya tauna ƙaya cikin sauƙi. 

Raƙumi yana da fatan idanu guda 2 masu bawa idanun shi kariya: 1 bashi da kauri siriri ne kuma ana ganin shi, 1 kuma yana da kauri kuma yana da tsoka. Lokacin da ƙura ta tashi a cikin sahara, Raƙumi 🐫 yana rufe fatan idanun shi mara kaurin domin hana ƙasa shiga, amma kuma duk da a rufe ne yana gani, fatar tana zama mishi kamar wani gilashin kariya kenan, Hakannan yana da dogon gashin idanu wanda suke hana ƙasa shiga cikin idanunshi.

Raƙumi yana da Ƙwarewar ƙwaƙwalwa wajen tantance nesa
Kwakwalwar raƙumi ta saba da binciken hoton da idon sa ya gani, don haka yana iya gane tsayin abu da tazara cikin sauri.

Wannan yana taimaka masa wajen gane tafarkin ruwa ko abinci a cikin hamada mai nisa.

Idanun raƙumi suna da ƙwayoyin gani (rods da cones) masu yawa wanda suke taimaka masa gani da kyau a lokacin dare wanda tamkar da rana yake gani.

Raƙumi yana iya kwanaki 7 zuwa 15 ba tare da yasha ruwa ba, sannan idan ya samu ruwa yakan sha sama da lita 100 

Haka kuma Raƙumi 🐫 yana iya lura da yanayin zafi ko sanyi na jikin shi wato (body temperature)..

Tsarki su ƙara tabbata ga Ubangiji, Allahu Maƙagin Ɗan Adam, Aljan, Dabba, Tsuntsaye, Shine wanda Bashi da farko balle ƙarshe.

Wannan fa kaɗan ne daga cikin baiwa da Ubangiji ya tara a jikin wannan dabba ta raƙumi.


SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: