Hakika wannan tsohuwar matan ta burge Mutane da dama saboda yadda aka ga tana karatun Alkur'ani Mai girma da kanta ba tare da wata matsala.
Yayin da zaka ga wasu tsofaffin a matakin shekarunta suna fama da laluran rafkannuwa da rashin gane abubuwa amma ita sai gashi tana karatu cikin natsuwa da murya mai Dadi.
Hakika hakan ya isa hujja game da karamar karantun Alkur'ani, domin duk Wanda yayi sa a lokacin kuruciyarsa kuma har ya tsufa bai bari ba zai samu natsuwar hankali da kwanciyar hankali fiye da na Wanda baya Karanta shi.
Allah ka bamu ikon cigaba da Karatun Alkur'ani har karshen rayuwarmu.
0 comments: