Thursday, August 14, 2025

Tarihin matan Annabi Muhammad SAW

Tarihin matan Annabi Muhammad SAW

A cikin wannan mukalar zaku Karanta tarihin matayen ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) Wanda ya aura a lokacin rayuwarsa da shekarun da suka rasu. Cikin matanShi su 12, biyu kawai daga ciki suka haihu, Nana Khadija (R.A) wacce ta haifi 'ya'ya 6 (Qasim, Zainab, Ruqayyah, Umm Kulthum, Fatima, Abdullah) sai Sayyada Mariyyah wacce ta haifi  da 1, Ibrahim.


1- Khadijah bint khuwailid

Nana Khadija ce matan manzon Allah ta farko wacce ya aura tun kafin Baiyanar Annabtanshi, sun haifi 'ya'yaye 6 tare, ta rasu shekaru 3 kafin hijran Manzon Allah (S.A.W) zuwa Madina inda aka binne ta a makabartar Jannat al-Mu'alla dake makka.


2- Saudat bint zam'ata. 

Saudat bin zam'ata (R.A), ita ce matar manzon Allah (S.A.W) ta biyu wacce ya aura bayan rasuwar Nana kadija (R.A). Ya aure ta ne bayan rasuwar mijinta As-Sakran ibn Amr a shekaran ta 3 kafin hijra, Sunan Dan ta Abdur Rahman ibn Sakran.

Sai dai bata haihu tare da manzon Allah ba Kuma tana daya daga cikin matan da manzon Allah (S.A.W) ya bari bayan wafatinSa.

Ta rasu a shekaran 22 bayan hijra inda aka binne ta a makabartar Al-Baqi dake Madina.


3- Aisha bint Abibakar

Nana Aisha (R.A) ce matar manzon Allah (S.A.W) ta 3 Kuma ita kadai ce wacce ya aura tana budurwa.

Nana Aisha (R.A) 'ya ce ga amininsa Kuma babban sahabinsa Sayyadina Abubukar (R.A).

Ya aure ta shekara ta 2 kafin hijra, ta rasu bayan wafatin ma'aiki (S.A.W) a shekara ta 56 bayan hijra.


4- Hafsat bint Umar. 

Sayyada Hafsat bint umar (R.A), ita ce matar Manzon Allah (S.A.W) ta 4 Kuma 'ya  ga babban sahabin Manzon Allah (S.A.W), Umar bin Khatab. 

Ta auri Manzon Allah (S.A.W) a shekara ta 3 bayan hijra, Kuma ta rasu bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W) a shekara ta 45 Bayan hijra.


5- Zainab bin khuzaimah.

Sayyada Zainab bin Khuzaimah ce matar Manzon Allah (S.A.W) ta biyar, ta auri Manzon Allah (S.A.W) bayan shahadar mijinta, Ubayda ibn al-Harith a yakin Badar a shekara ta 2 bayan hijra.

Sai dai ita ma ta rasu a shekara daya bayan auren inda aka binne ta a makabartar Jannat al-Baqi dake birnin madina, ana yi mata lakabi da Umm al-Masakin, wato uwar Talakawa.


6- Ummu Salmah.

Ita ce matar da Manzon Allah (S.A.W) ta 6 wacce Ya aura Bayan rasuwar mijinta Abu salmah a shekara ta 2 bayan hijra.

Sunanta Hind bint Abi Umayya Amma ana Mata lakabi da Ummu salmah, wato uwar Salamah, daya daga cikin 'ya'yayen da ta Haifa da Abu Salmah Wanda suka hada (Salama, Umar, Zaynab da Ruqayyah).

Ummu salmah da Abu salmah na daya daga cikin wadanda suka fara karban musulunci inda suka fuskanci kunci da takura daga wajen Kafiran Makkah.

Ta rasu a shekara ta 62 bayan hijra inda aka binne ta a makabartar Jannat al-Baqi.


7- Zainab bint jahshin. 

Ita ce matar Manzon Allah (S.A.W) ta 7 wacce ya aura bayan tsohon mijinta Kuma Sahabin Manzon Allah (S.A.W), Zayd ibn Harithah ya sake ta a shekara ta 5 bayan hijra.

Sayyada bint jahshin 'yar uwa ce ga Manzon Allah (S.A.W) ta bangaren mahaifinShi, Sayyadi Abdullah (A.S), ita Sayyada Zainab (R.A) 'ya ce ga Umaymah bint ʿAbd al-Muṭṭalib, wacce suke mahaifiyarsu daya da mahaifin Manzon Allah (S.A.W), Sayyadi Abdullah (A.S).

Ta rasu a shekara ta 19 bayan hijra Inda aka binne ta a makabartar Jannat al-Baqi dake birnin madina.


8- Juwairiyya bint Al-haris. 

Ita ce matar Manzon Allah (S.A.W) ta 8, wacce ya aura a shekara ta 5 bayan hijra bayan rasuwar mijinta Mustafa ibn Safwan a wajen yaki.

Ta na daya daga cikin matan da suka rayu da manzon Allah (S.A.W) har lokacin wafatinSa.

Bata saru ba sai a shekara ta 54 bayan hijra.


9- Ummu habibah.

Ummu Habibah wacce cikakken Sunanta shine Ramla bint Abi Sufyan ibn Harb, ('yar Abu safyan) ita ce matar Manzon Allah (S.A.W) ta 9 wacce ya aura bayan rasuwar mijinta Ubayd Allah ibn Jahsh a shekara ta 6 bayan hijra.

Ana Mata lakabi da Ummu Habibah ne wato uwar Habibah, 'yar da ta haifa da tsohon mijinta, Ubayd Allah ibn Jahsh.


10- Safiyyah bint huyay. 

Sayyada Safiyyah 'yar kabilar Banu Nadir ce wacce manzon Manzon Allah (R.A) ya aura bayan ta musulunta bayan yakin Khaibar.

Ta rasu a shekara ta 42 bayan hijra.


11- Maimunah bint Al-haris.

Cikakken Sunanta shine Maymuna bint al-Harith al-Hilaliyya, ita ce mace ta 11 da Manzon Allah ya aura a shekara ta 7 bayan hijra, Kuma ta rasu bayan wafatin ma'aiki (S.A.W) da shekara 39.


12- Maria al-Qibtiyya.

Sunanta Māriyya bint Shamʿūn al Qibtiyyah Amma ana Mata lakabi da Maria al-Qibtiyya, ta auri Manzon Allah (S.A.W) a shekara ta 6 da hijra Kuma ita kadai ce matar da ta haihu da Manzon Allah (S.A.W) bayan Nana Khadija, inda ta haifi Ibrahim (A.S) sai dai ya rasu tun yana da shekara 2 a duniya a shekaran da Annabi (S.A.W) yayi wafati.

Ita ma Sayyada Mariya ta rasu shekaru biyar bayan wafatin ma'aiki (S.A.W).



SHARE THIS

Author:

I am a personal blogger by experience, interesting in creativity, learning new things and sharing Islamic contents for the benefit of Muslim ummah.

0 comments: