Saturday, July 19, 2025

Sheikh Muhammad Auwal: Fadakarwa akan masu taba Janibin iyayen ANNABI (S.A.W)


Sheikh Muhammad Auwal yaja hankalin Malamai masu wa'azi game da kiyaye harsunansu wajen kafirta 'yan uwansu musulmai da Kuma masu taba Janibin iyayen fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMAD (S.A.W).

A cikin wannan bidiyon dake kasa shehun malamin yayi nuna takaicinsa game da yadda yace yaji wani malamin addinin musulunci a Najeriya Yana ikirarin cewa iyayen ANNABI (S.A.W) 'yan wuta ne (wa'iyazubillah),inda yace sai da yayi kuka da yaji wannan kalma daga bakin Wanda ke ikirarin daawa.
Inda ya kara da cewa kwakwata bai kamaci mai wa'azi ba ya rinka kafirta wani domin yin hakan ba koyarwar musulunci bane.

Ku latsa wannan bidiyon domin sauraron cikakken jawabin daga bakin Sheikh Muhammad Auwal mazaunin kasar Amurka.




SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: