Saturday, June 14, 2025

Yakini da Allah cewa babu Wanda zai iya cutar dakai sai ya kaddara hakan

Yakini da Allah cewa babu Wanda zai iya cutar dakai sai ya kaddara hakan


Hakika duk mumini yakamata ya samu yakini a zuciyarsa cewa babu wani mahaluki daga halittan ubangiji da zai iya cutar da shi sai idan Allah ya kaddara samuwar hakan.

Domin rayuwar muminai ta dogara ne kacokan akan yin biyayya ga Allah madaukakin sarki da manzonsa, don haka Allah madaukakin sarki yayi Alkawari ga duk wanda yayi masa da'a yayi wa manzonsa da'a zai jibinci lamuransa.

Kamar yadda yazo a cikin wannan hadizin da Ibn Abbas (RA) ya ruwaita inda Manzon Allah (S.A.W) yace:

"Ka sani cewa da duk duniya za su taru a kan ka don su cutar da kai, ba za su iya cutar da kai ba face da abin da Allah ya riga ya rubuta."

Wannan hadisi yana karantar da mu cikakken tawakkali ga kadaran Allah, babu abin da zai taba samunka face Allah ya riga ya rubuta shi a cikin kaddaran ka. 

Ko da dukan rundunonin Shaiɗan da abokansa na ’yan Adam, zasu taru domin yi maka makirci, ba zasu iya cutar dakai ba sai da izinin ubangiji.

Article Translation in English Language.

Hadith: “Know that if the entire world were to gather against you to harm you, they could not harm you except with what Allah (swt) has already decreed.”

This hadith is from a narration by Ibn Abbas (رضي الله عنه), where the Prophet ﷺ said:

This hadith teaches absolute reliance on Allah’s Qadr (Divine Decree)—nothing can touch you unless Allah has already written it in your fate. Even if all of Satan’s forces, his human allies, and his whispers conspire against you, they have no independent power.


SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: