Wani babban malamin Addinin musulunci mabiyin akidar salafiyya ya bayyana cewa kasar Iran ce gatar musulmi a halin yanzu.
Yayi jawabin ne sakamakon yakin da ya barke tsakanin Kasar Iran din da haramtacciyar kasar Israi'la a ranar juma'a da ta gabata bayan Israi'la ta kaddamar da hare-hare a kan cibiyoyin tashar makamin Nukiliyan Iran Wanda yayi sanadin rasuwar manyan kwamandojin Sojin kasar Iran uku.
Duk da cewa har zuwa lokacin da nake wannan rubutun ban da masaniyar sunan wannan malamin, Amma ya dace in kawo maku wannan bidiyon domin ku amfana daga jawaban da yayi masu muhimmanci da sosa zuciya.
Malamin yayi bayanin cewa duk da cewa suna da banbancin akida 'yan Shi'a wadanda sune mafiya yawan Al'ummar a kasar ta Iran, Amma komin kin Allahn ka da kin gaskiyarka a duniyar da muke cikin a halin yanzu sun zama gata wa musulunci kuma sun zama gata wa musulmai.
Don haka mu maganar musulunci muke yi ba maganar akida ko mazhabanci ko kungiyanci ba. Inji malamin.
Latsa wannan bidiyon dake kasa domin kallon cikakken jawabin.
0 comments: