A cikin wannan hadisin zamu ga yadda Allah madaukakin sarki ya ke nuna rangwame ga bayinsa wajen fifita aiyukan alkairansu akan munana.
Domin Allah (S.W.T) Mai Rahama da gafara ne ga bayinsa.
Don haka dan uwa kada kaga wani ya shagala da mummunan aikin zunubi a maimakon kayi masa fatan shiriya sai ka rinka la'anarsa da yin mashi mummunar fata, yin hakan ba koyarwar musulunci bane domin ta yuyu Allah ya gafarta mashi dukkan zunubanshi dalilin aikinsa daya na alkairi.
Zamu Kara samun darasi kwarai idan muka dubi Rahamar Allah da falalar shi a cikin wannan hadisin na 37 daga cikin littafin Arba'una Hadith Wanda Imam Nawawi ya rubuta.
Karanta Fassarar Hadisi na 37 daga cikin littafin Arba'una Hadith.
An karbo daga Ibn Abbas (Allah Ya yarda da shi), daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), daga abin da ya ruwaito daga Ubangijinsa:
Yace: Lallai Allah Ta’ala yana rubuta ayyukan alheri da munanan ayyuka, sa’an nan ya yi bayaninsa [da cewa]:
“Duk wanda ya yi nufin aikata alheri, amma bai aikata ba, to, Allah Yana rubuta shi ladan matsayin aikin alheri cikakke, haka zalika idan ya yi nufin ya aikata Alkairi, sa’an nan ya aikata, sai Allah Ya rubuta mashi da kansa daga ayyuka goma na alheri har sau dari bakwai.
Haka zalika idan yayi nufin aikata mummunar aiki sai kuma bai aikata ba, sai Allah ya rubuta mashi cikakken ladan kyakkyawan aiki, kuma idan ya yi nufin mummunan aiki sa’an nan kuma ya aikata shi, sai Allah Ya rubuta mashi zunubi daya a matsayin aiki na mummuna.
[Bukhari da Muslim]
Article Translation in English Language.
On the authority of Ibn Abbas (may Allah be pleased with him), from the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him), from what he has related from his Lord:
Verily Allah ta’ala has written down the good deeds and the evil deeds, and then explained it [by saying]: “Whosoever intended to perform a good deed, but did not do it, then Allah writes it down with Himself as a complete good deed. And if he intended to perform it and then did perform it, then Allah writes it down with Himself as from ten good deeds up to seven hundred times, up to many times multiplied. And if he intended to perform an evil deed, but did not do it, then Allah writes it down with Himself as a complete good deed. And if he intended it [i.e., the evil deed] and then performed it, then Allah writes it down as one evil deed.”
[Bukhari & Muslim]
عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صلى الله عليه و سلم فِيمَا يَرْوِيهِ عَنْ رَبِّهِ تَبَارَكَ وَتَعَالَى، قَالَ:
"إنَّ اللَّهَ كَتَبَ الْحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ، ثُمَّ بَيَّنَ ذَلِكَ، فَمَنْ هَمَّ بِحَسَنَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا كَتَبَهَا اللَّهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا كَتَبَهَا اللَّهُ عِنْدَهُ عَشْرَ حَسَنَاتٍ إلَى سَبْعِمِائَةِ ضِعْفٍ إلَى أَضْعَافٍ كَثِيرَةٍ، وَإِنْ هَمَّ بِسَيِّئَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا كَتَبَهَا اللَّهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا كَتَبَهَا اللَّهُ سَيِّئَةً وَاحِدَةً".
[رَوَاهُ الْبُخَارِيُّ] ، [وَمُسْلِمٌ]، في "صحيحيهما" بهذه الحروف.
0 comments: