Hadisi na 36 dake cikin Arba'una hadith na imam annawawi yana dauke da darusa masu tarin yawa game da kyautata ma 'yan uwanmu musulmai a cikin lamuranmu.
Misali ,Duk musulmin kwarai yakamata ya kasance mai tausayin dan uwansa musulmi ta hanyar taimakama mashi idan ya shiga mayuyacin hali da kuma rufa mashi asiri domin kare mutuncinsa a idanun jama'a.
Haka zalika hadisin yayi bayani game da falalar neman ilimi ga musulmi, inda Allah madaukakin sarki yayi alkawarin saukaka ma duk Wanda ke neman ilimi hanyar shiga Aljanna.
Kuma Allah madaukakin sarki ya yi alkawarin saukar da natsuwa ga zuciyoyin bayinSa wadanda suka kasance suna ambatonSa ta hanyar yin zikiri da karatun Alkur'ani tare da lullubesu da rahamarSa da jin kanSa tare da ambatonsu a matsayin wadanda suke tare da SHI.
Hakika wannan wata falalace da babu wanda ya isa ya same ta in ba Al'ummar Annabi Muhammad (S.A.W) ba.
Karanta Fassarar Hadisi na 36 daga cikin Arba'una Hadiths:
An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce:
Manzon Allah (SAW) ya ce: Wanda ya kankare baqin cikin duniya daga mumini, Allah zai kankare masa baqin cikin ranar qiyama.
Kuma duk wanda ya saukaka buqatar mabuqaci, Allah zai saukaka masa buqatarsa a duniya da Lahira.
Duk wanda ya yi garkuwa (ko boye munanan ayyukansa) musulmi, Allah zai kare shi duniya da lahira.
Kuma Allah zai taimaki bawansa matukar ya taimaki dan uwansa.
Kuma wanda ya bi hanya domin neman ilimi a cikinta, Allah zai sauwake masa hanyar shiga Aljannah.
Babu wasu mutane da zasu taruwa a waje daya daga cikin dakunan Allah suna karatun littafin Allah suna karantar da shi a tsakaninsu, face sai sakeenah (natsuwa) ta sauka a gare su, kuma rahama ta lullube su, kuma mala'iku sun kewaye su, kuma Allah ya ambace su a cikin wadanda suke tare da shi.
Kuma duk wanda ayyukansa suka sassauta masa, to ba za su gaggauce da zuriyarsa ba.
[Muslim ya ruwaito]
Article Translation in English Language.
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), that the Prophet (peace be upon him) said:
Whoever removes a worldly grief from a believer, Allah will remove from him one of the griefs of the Day of Resurrection.
And whoever alleviates the need of a needy person, Allah will alleviate his needs in this world and the Hereafter.
Whoever shields [or hides the misdeeds of] a Muslim, Allah will shield him in this world and the Hereafter.
And Allah will aid His slave so long as he aids his brother.
And whoever follows a path to seek knowledge therein, Allah will make easy for him a path to Paradise.
Hadith no 36 of Arba'una Hadiths in Arabic language.
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنْ النَّبِيِّ صلى الله عليه و سلم قَالَ:
"مَنْ نَفَّسَ عَنْ مُؤْمِنٍ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ الدُّنْيَا نَفَّسَ اللَّهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ يَسَّرَ عَلَى مُعْسِرٍ، يَسَّرَ اللَّهُ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَمَنْ سَتَرَ مُسْلِما سَتَرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ، وَاَللَّهُ فِي عَوْنِ الْعَبْدِ مَا كَانَ الْعَبْدُ فِي عَوْنِ أَخِيهِ، وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقًا يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْمًا سَهَّلَ اللَّهُ لَهُ بِهِ طَرِيقًا إلَى الْجَنَّةِ، وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ اللَّهِ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ، وَيَتَدَارَسُونَهُ فِيمَا بَيْنَهُمْ؛ إلَّا نَزَلَتْ عَلَيْهِمْ السَّكِينَةُ، وَغَشِيَتْهُمْ الرَّحْمَةُ، وَ حَفَّتهُمُ المَلاَئِكَة، وَذَكَرَهُمْ اللَّهُ فِيمَنْ عِنْدَهُ، وَمَنْ أَبَطْأَ بِهِ عَمَلُهُ لَمْ يُسْرِعْ بِهِ نَسَبُهُ".
[رَوَاهُ مُسْلِمٌ] بهذا اللفظ.
0 comments: