Thursday, June 5, 2025

Falalar Azumin Litinin da Alhamis a musulunci

Falalar Azumin Litinin da Alhamis a musulunci

Azumin Litinin da Alhamis Azumin nafila ne da ake yi domin yin koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) Wanda ya kasance yanayi a lokacin rayuwarsa.

Ga wasu hadisai da aka ruwaito wadanda ke nuna inganci wannan Azumin na Litinin da Alhamis.

Daga A'isha uwar muminai (RTA) tace'; Manzon ALLAH ﷺ yana yin azumin Litinin da Alhamis. 

[Saheehut tirmidhi]


Daga Abi sa'idil hudriy (RTA) daga Manzon ALLAH ﷺ yace'; Manzon ALLAH ﷺ yace' duk wanda yayi azumin wuni ɗaya saboda ALLAH, ALLAH zai nesantar da fuskar sa daga wuta sau ninki saba'in. 

[Muslim ya ruwaito]


Daga Abi Hurairah (RTA) Manzon ALLAH ﷺ Yace'; Ana bijiro da ayyukan bayi ranar Litinin da Alhamis sai na qaunaci a bijiro da ayyuka na ina azumi.

[Saheehut tirmidhi]


Daga Abi Hurairah (RTA)  Manzon ALLAH ﷺ Yace'; A cikin ALJANNAH akwai kofofi guda takwas, a cikin ta (aljannah in) akwai wani kofa sunan ta RAYYAN, babu masu shigar ALJANNAH ta wannan kofar sai masu azumi. 

[Bukhari ya ruwaito]

Imamun nisa'i ya kara da cewa'; idan na ƙarshen su (masu azumi) ya shiga sai a kulle kofar, wanda ya shiga cikin ta akwai wani abun sha, duk wanda yasha kuma ba zai sake jin kishi ba har abada. 

Manzon ALLAH (S.A.W) yace; "ALLAH Yana cewa Azumi nawa ne, ni ne zan saka da shi (Ni zan bada ladan sa), wanda yake azumi yana barin sha'awar sa, cin sa, da shan sa saboda ni, kuma azumi kariya ne kuma mai azumi yana da farin ciki guda biyu; farin cikin lokacin da yake buɗa baki, da farin cikin lokacin da yake haɗuwa da UBANGIJIN sa, kuma warin baki mai azumi a wurin ALLAH yafi almiski kamshi.

[Bukhari, Muuslim, Malik, Tirmidhi, Nisa'i da ibn majah ne suka rawaito.

Article Translation in English Language.




SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: