Addinin musulunci addini ne da ya baiwa kowa hakkinsa, babu cuta ko cutarwa a cikinsa, daga cikin irin wadannan hakkoki da musulunci ya dora wa mabiyansa, akwai hakkin miji a kan matarsa, da hakkin mata a kan mijinta.
Hakika sanin wadannan hakkoki, abu ne mai matukar mahimmanci ga ma'aurata, saboda idan miji ya san hakkin matarsa a kansa, ita ma mata ta san hakkin mijinta a kanta, zaman aure zai yi dadi, za a samu nutsuwa da kwanciyar hankali, da kyakkyawar zamantakewan aure, a zasu yi rayuwa mai dadi a duniya, a kuma samu kyakkyawan sakamako a ranar lahira.
Saboda haka wannan takaitaccen jawabi zai kunshi bayani ne game da hakkokin miji a kan matarsa da hakkokin mata a kan mijinta.
HAKKOKIN MIJI A KAN MATARSA
Miji yana da hakkoki a kan matarsa, wadanda ya wajaba ta kiyaye da su, kuma ta sauke nauyinsu, Allah Madaukakin Sarki ya ce :
“Su ma (mata) suna da kwatankwancin abin da yake kansu da adalci, maza kuma suna daraja a kansu, Allah Mabuwayi ne Mai Hikima”. (Al-baqara : 228).
Imam Ibnu Kasir – Allah Ya jikansa da rahama – ya ce :
“Fadin Allah cewa “Suma (mata) suna da kwatankwacin abin da yake kansu da adalci” ma’ana suma (mata suna da hakki a kan maza, irin hakkin da maza suke da shi a kansu, don haka kowa ya baiwa dan uwansa hakkinsa da adalci..”.
Hakkokin Miji akan matarsa suna da yawa, kuma suna da girma, saboda haka Manzon Allah (S.A.W) yake cewa :
“Hakika ni da zan umarci wani ya yi sujjada ga wanin Allah, da na umarci mace ta yi wa mijinta sujjada. Na rantse da wanda ran Muhammad yake hannunsa, mace ba zata biya hakkin Ubangijinta ba, har sai ta bayar da hakkin mijinta, kuma da zai tambaye ta kanta, alhali tana kan siddin raqumi da baza ta hana shi ba” Imam Ahmad da Ibnu Majah da Ibnu Hibban ne suka raiwaito shi.
Daga cikin hakkokin miji a kan matarsa, wadanda ya wajaba ta kiyaye su, kuma ta sauke su, akwai :
1 – Yi masa biyayya : Musulunci ya umarci mace ta yi wa mijinta biyayya cikin abin da bai sabawa Allah Madaukakin Sarki da Manzon Allah (S.A.W) ba.
Ya inganta a cikin hadisin Abu Hurairata (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Idan Mace ta sallaci biyar din ta, ta azumci watanta (wato Ramadan) ta kiyaye farjinta, ta yi wa mijinta biyayya, za ta shiga Aljannah daga kofar da taga dama daga cikin qofofin Aljannah”.
Biyayyar mace ga mijinta wajibi ce, kuma idan mace ta saba wa mijinta, ta ki yi masa biyayya, to zata wayi gari a cikin fushin Allah, har sai mijinta ya yarda da ita, ya daina fushi da ita.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa wata mata :
“Ki duba, meye matsayinki a wurin (mijinki), domin shi ne Aljannarki ko wutarki”. Nisa’i da Hakim da Dabarani da waninsu suka rawaito shi.
2 – Biya Masa Bukatar Aure : Wajibi ne akan mace ta biya wa mijinta buqatarsa ta aure, ta amsa masa a duk lokacin da ya bukace ta, Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Idan mutum ya kira matarsa zuwa ga shimfidarsa, ba ta zo ba, ya kwana yana mai fushi da ita, to Mala’iku za su la’ance ta, har sai ta wayi gari”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Sai dai baya halatta mace ta yi wa mijinta biyayya wajen kwanciyar aure in tana tare da wani uzuri da shari’a ta yarda da shi, kamar idan tana cikin jinin al’ada ko biki, ko kuma in tana azumin farilla, ko idan ya neme ta dubura, ko yayin da take cikin aikin hajji ko umara, da sauransu, saboda yarda da haka sabawa Allah ne Madaukakin Sarki, kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Babu da’a ga wanin abin halitta cikin saba wa mahalicci”.
HAKKOKIN MATA AKAN MIJINTA.
Hakkokkin mata akan mijinta sune:
Ciyarwa da shayarwa
Kula da lafiyarta
Kula da iliminta
Kula da tarbiyarta.
Wajibin miji ne ya kula da dukkan abun da ya shafi ciyarwar matarshi daidai da yadda karfin wadatarsa yake, Babu adalci ga magidancin da yake da wadata amma yabar iyalansa Suna rayuwa irin cikin kunci na rashin kulawa da ciyarwa.
Haka zalika wajibin miji ne ya kula da duk wani dawainiya na rashin lafiya da ya shafi matarsa
Ilmantarwa shima Wani hakki ne da miji ya wajaba ya tabbatar matarsa ta samu kulawa daga wajensa domin shine zai zame mata fitila ga rayuwar aurenta.
Tarbiya abune da baya kare wa, wajibin miji ne ya tabbatar Yana kula da mu'amalar matarsa, ta hanyar bata shawarwari da nasiha akan abubuwan da zasu amfane ta da Kuma tabbatar da bata mu'amala da bata Garin kawaye masu bata gurguwar shawarwari.
Article Translation in English Language.
The religion of Islam is a religion that gives everyone their rights, there is no disease or harm in it, among the rights that Islam has imposed on its followers, there is the right of a husband over his wife, and the right of a woman over her husband.
Of course, knowing these rights is very important for married couples, because if the husband knows his wife's rights on him, the wife also knows her husband's rights on her, the marriage will be happy, there will be peace and stability, and a good marriage relationship, they will live a happy life in this world, and get good results in the hereafter.
Therefore, this short speech will contain information about the rights of a husband over his wife and the rights of a woman over her husband.
HUSBAND'S RIGHTS ON HIS WIFE A husband has rights over his wife, which he is obliged to protect and discharge their responsibilities, God Almighty said:
"They (women) also have a comparison of what is right for them, and men have respect for them. God is Almighty, Wise." (Al-Baqara: 228).
Imam Ibnu Kasir - may God have mercy on him - said:
"God's word that "They (women) also have the same rights as themselves and justice" meaning they also (women) have rights over men, the same rights that men have over them, so everyone should give his brother his rights and justice..".
The rights of a husband over his wife are many, and they are great, therefore the Messenger of God (S.A.W) says:
"Indeed, I would order someone to prostrate to other than Allah, I would order a woman to prostrate to her husband.
I swear by the one in whose hands is the life of Muhammad, a woman will not pay the rights of her Lord, until she gives the rights of her husband, and if he asks her herself, while she is on the saddle of a camel, she will not prevent him" It was narrated by Imam Ahmad, Ibnu Majah and Ibnu Hibban.
Among the rights of a husband over his wife, which he is obliged to protect and to discharge, there are:
0 comments: