Aure ibada ce Kuma Sunnan Manzon Allah (S.A.W), ana daura aure ne bisa ginshikin yarda da juna (Soyayya) a matsayin Abokan zama na har abada.
Bisa koyarwar Musulunci Aure baya halatta sai da yardar magabata (waliyai) daga bangaren namiji da mace, sannan sai sadaki.
Kuma addini yayi umurni a duk lokacin da mutum zai nemi aure ya nemi ma'abociya addini ce ba domin addini shine ginshikin rayuwar Dan Adam.
Aure ba wajibi bane ga namiji ko mace matukar dukkanninsu zasu iya kame kawunansu daga fadiwa alfasha, sai dai zamu iya cewa duk Wanda bai yi aure ba ya rasa babban lada da falalar dake cikinsa Wanda manzon Allah (S.A.W) kwadaitar da mu.
Sai dai a cikin wannan Karnin Al'ummar Musulmi musamman wadanda ke arewacin najeriya na fuskar yawan mace-macen aure da Wanda ke yin mummunar illa ga cigaban yankin.
Saboda a cikin wannan mukalar zamu kawo wasu abubuwa da suke taka muhimmiyar rawa wajen mutuwar aure musamman a kasar Hausa, (arewacin najeriya).
Ga wasu daga cikin su kamar haka:
1. Rashin sanin daraja da hakkokin aure
2. Kaucewa koyarwar Manzon Allah game da zamantakewar ma'aurata
3. Girman kai ga maza, rashin kunya ga mata
4. Yin aure saboda kawai don sha'awa, dukiya ko wani son abin duniya
5. Karin aure yayin da babu ikon yi
6. Rashin adalci da wulakanta abokin zama
7. Rashin bin ka'idojin saki
8. Jahilci
9. Rashin son haihuwa
10. Baiwa al'adu muhimmanci fiye da addini
11 Zargi a tsakanin ma'aurata
Article Translation in English Language.
Marriage is an act of worship and the Sunnah of the Messenger of God (S.A.W), marriage is based on mutual trust (Love) as eternal companions.
According to Islamic teachings, marriage is not permissible except with the consent of the elders (saints) from the male and female side, and then dowry.
And religion commands every time a person wants to marry and seek a lover, it is not religion because religion is the foundation of human life.
Marriage is not obligatory for a man or a woman as long as they can control themselves from falling into adultery, but we can say that anyone who is not married has lost the great reward and grace that the married people gaining.
However, in this century, the Muslim community, especially those in the north of Nigeria, are facing a high rate of marriage deaths, which is causing serious harm to the development of the region.
So in this article we will bring some things that play an important role in the death of marriage especially in Hausa country (northern Nigeria).
0 comments: