Friday, April 18, 2025

Tarihin Annabin Allah: Annabi Ayuba (A.S)

InshaAllah yau zamu kawo muku kissar

Annabi Ayuba (AS) ne da irin yadda rayuwar sa ta kasance da irin hakurin da ya yi na tsawon shekaru game da jarabawar da Allah Madaukakin sarki ya saukar masa na Rashin lafiya.

Annabi Ayuba (AS) yana daga cikin fittatun Annabawan Allah guda 25 da Allah ya ambaci sunan su a cikin alkur'ani mai girma, An ambaci sunanshi har sau 4 a cikin Alkur'ani, a cikin surori guda 4, a ayoyi guda 4. 

kuma sunansa Ayub ya samo asali ne daga Aba, Yub wato wanda aka sake dawo masa da lafiya da ni'ama da dukiya da ya'ya' bayan da aka amshe su. 

har ila yau Annabi Ayyub (A.S) ya kasance daga cikin 'yayan Annabi Ibarahim (AS) kamar yadda masana Tarihi suka bayyana nasabarsa inda suka nuna cewa Ayuba bin Amus bin Razij, bin Rum, bin Isa, bin Ishaq bin Ibrahim. Kuma Mahaifiyar sa tana daga cikin yayan Annabi Ludu bin Harran (A.S). 

To sai dai masu saurare zasu so sanin a ina ne hakikanin mahaifar Annabi Ayuba (AS).

An Samu Sabani tsakanin malaman tarihi game da hakinin mahaifar sa,

inda wasu suka bayyana cewa an haife shi ne a garuruwan Basana, Iwada, Jabiyya, dake garin Sham a birnin Damaskas na kasar Siriya, kuma an haife shi ne bayan shekaru 3642 da saukar Annabi Adam (A.S) a doran duniya. 

Kuma ya koma ga Allah ne yana da shekaru 93 da haihuwa a duniya kuma kabarin sa yana kan kololuwar dusten jihaf ne dake da tazarar mil 80 da iyakar kasar Yaman da garin Adnan, Wani Marubucin littafin Tarihin Bal'ami ya fadi cewa Annabi Ayuba (AS) ya rayu ne a wani gari mai suna Basneh dake kewayen kasar sham, kuma ya kwashe shekaru 7 yana ibada da neman kusanci ga Allah tare kuma da cigaba da kiran Al'umma zuwa ga hanyar gaskiya na Kadaita Allah, amma mutane 3 ne kawai sukayi Imani dashi. 

Ya kasance daga cikin Annabawan da akayi bayanin rayuwar su filla- filla acikin Alkur'ani mai girma ya kasance yana tausayawa marayu da marasa galihu da makafi dama wadanda basu da wanda ke kula da su, kuma ya shahara a garin wajen tarbar baki tare da basu masauki da kuma kyautata masu.

Annabi Ayuba (AS) ya kasance yana da dukiya mai yawa kuma ya kasance yana kiwo inda yake da dabbobi da tsuntsaye masu yawa, kuma yana da manya - manyan gonaki da yake noma a cikin su, to sai dai bayan da aka dauki dogon zamani sai dukkan gonaki da dukiyoyin da dabbobin daya mallaka suka kare, kuma aka jarabce shi da jarabobi masu yawa ciki har da matsananciyar rashin lafiya wanda babu abinda ya rage a jikinsa banda zuciyar sa da harshen sa da yake ambaton Allah dashi amma duk jikin sa cututtuka ne, amma duk da haka ya kasance mai hakuri na tsawon lokacin da ya dauka yana rashin lafiya, kuma bai taba yin raki ko nuna gazawa ko gajiyawa ba. 

Hakaki Annabi Ayuba (As) ya dauki dogon lokaci yana fama da rashin lafiya har ya kai ma babu wanda ke zama a wajen sa, tun ana zuwa a gaida shi har ya kai mutane baki daya sun dauke kafa daga wajen shi baki daya. 

Wanda saboda tsananin rashin lafiyar da yake ciki babu wanda ke magana dashi daga karshe ma ya yanke shawarar ficewa daga wannan garin, ya koma bayan gari ya zauna a bukka wanda hakan yasa dukkan mutanen garin suka yanke duk wata alaka dake tsakanin su dashi, Babu wanda ya kula da hakkinsa a cikin al'ummar garin sai matarsa kawai, kuma Itace kawai tasan kimar irin kyautatawar da yayi mata domin basa nuna masa tausayi da soyayya da ya kamata su nuna masa. 

Matarsa itace kawai take kai kawo a wajen sa, inda da kullum da sassafe takan je ta tsaftace wajen da yake kwance ta gyara kayan sa kuma ta tsaftace masa jikinsa, duk kuwa da rauni da take dashi da rashin kudi, wanda ya hakan yasa take zuwa tayi wa mutane aikin kwadago kafin ta samu kudin da za ta tanadarwa da mijinta abincin da zai ci. 

Kuma ta cigaba da hakuri da wannan yanayi da take ciki ba tare da gajiyawa ba. 

Duk da irin jin dadin da ya kasance a ciki da fari da kuma irin dukiya da yake dashi kana daga bisani ya rasa dukkan abinda da ya mallaka. 

Allah ya jarabce shi da rashin lafiya da kuma irin halin da ya fada tare da matar sa na talauci, da fatara, Annabi Ayyuba (AS) yayi hakuri babu abin da yake yi banda godiya ga mahallicin sa, irin wannan matsayi da Annabi Ayuba (AS) ya kai ya zama abin koyi da buga misali ga sauran al'ummomi da suka zo bayan sa, kamar yadda mahawallafin littafin Bidaya Wannihaya ya kawo acikin littafin sa mujalladi na 1 daya cewa:

wata rana Matar Annabi Ayuba (AS) ta taba tambayar sa cewa ashe baza ka gabatar da bukatar ka a wajen Ubangijin ka ba domin ya yaye maka wannan rashin lafiya da take Addabar ka? 

sai ya bata amsa da cewa na kwashe shekaru 70 ina cikin koshin lafiya ina gudanar da rayuwata a cikin walwala da jin dadi, don haka don nayi hakuri game da shekaru 7 kawai da wannan hali da nake ciki baiyi kadan ba?. 

Sai dai masana suna da sabanin game da tsawon lokacin da Annabi Ayuba (A.S) ya dauka yana rashin lafiya wasu sun bayyana cewa shekaru 30 ya kwashe yana rashin lafiya wasun su kuma suka ce shakaru 7 ya kwashe yana fama da rashin lafiya, inda wasu ma suka ce watanni ne kawai, wasu kuma suka ce shekaru 18 ne.

Allah ne masanin hakikan lokacin, amma Ko Shakka babu hakuri da nuna godiya ga ubangiji da Annabi Ayuba (as) yayi abin koyi ne ga dukkan talikai kamar yadda yazo a cikin Alkur'ani mai girma Allah ya siffata Annabi Ayuba (A.S) a matsayin daya daga cikin manyan bayin sa, kuma ya

bayyanashi a mastayin mai hakuri kuma yana da ga cikin zababbu kuma ya na daga cikin bayin sa salihai nagari kuma abin koyi ga dukkan Al'ummar duniya baki daya. 

Tarihin Annabi Ayuba (AS) yana nuna cewa hakika ya kasance cikin rashin lafiya da wahala da tsakanin har na shekaru 7 zuwa 18 a rayuwar sa, inda mutanen sa suka yanke duk wata dangantaka tsakanin su da shi saboda tsananin rashin lafiya da yayi fama da shi, matar sa ce kawai ta kasance tana tare dashi ta rike alkawari amma sauran dangin sa babu abin da ke tsakanin shi da su banda aibantawa da tuhume -tuhume, a cikin Alkur'ani anyi maganar Annabi Ayuba (AS) a yoyi 12 ne duk kuwa da yake cewa sau 4 ne kawai aka ambaci sunan shi a cikin alkur'ani din. 

Domin Alkur'ani yayi bayani a fili cewa hakika Allah ya Jarabci Annabi Ayuba da rashin lafiya. 

Sai dai daga bisani ya roki Allah madaukakin sarki game da halin da yake ciki inda aka amsa Addu'ar sa a ka yaye masa rashin lafiyar da yake fama da ita, kuma aka dawo masa da dukkan iyalansa, sai dai akwai aya babba game da yadda Allah Madaukakin sarki ya warkar da rashin lafiyar da Annabi

Ayuba yayi fama da ita, inda Allah. yake cewa 

"ya kai Ayuba ka goga kafafun ka a kasa, nan take Ayuba ya aikata abinda aka umarce shi sai kawai ga ruwa mai sanyi yana bulbulowa daga karkashin kafafunsa bayan nan sai Allah ya umarce shi da ya

wanke jikinsa da wannan ruwan kuma yasha daga gare shi, bayan

da ya aikata haka nan take sai kawai Allah ya yaye masa dukkan

zafi da radadin jiki da yake ji"

Allah ya yaye masa dukkan cututtukan dake damun sa a jikin sa na zahiri da badini.

Ustaz mustapha muragi acikin tafsirin sa ya fadi cewa a nan an bayyana irin cutar da Annabi Ayuba yake fama da ita ne, wato wata cuta ce ta fata wadda kuraje suke fitowa kamar karzuwa wanda ke sawa

mutum ya rika susa ya na kar tan jikinsa, wanda ke sawa jikin

mutum yana zafi da radadi.

Yazo a cikin ruwaya cewa wata rana shedan ya je wajen matar Annabi Ayuba (AS) a siffar mai magani sai yace mata zai warkar mata da mijinta amma da sharadin idan har ya warke zatace lallai shi kadai ne kawai ya warkar mata da

mijinta, bayan haka baya bukatar wani sakamako da ga gare ta, to sai dai saboda irin tsananin damuwar da matar Annabi Ayuba take ciki game da rashin lafiyarsa ya sa ta amince da wannan shawara da shedan ya bata da ya fito mata a siffar likita don haka sai taje wajen Annabi Ayuba (AS) ta shaida masa wannan shawarar sai dai lokacin da ta bayyana masa sai ya fahimci lallai tarkon shedan ne

amma saboda yadda yaga matar sa ta cije akan ra'ayinta sai ya

bayyana mata cewa ya yarda amma ya rantse cewa idan har aka

dawo masa da lafiyar sa ya warke to zai yi mata bulala 100 domin

ya ladabtar da ita akan dagewar da tayi, don haka lokacin da

Annabi Ayuba ya warke kuma don ya cika rantsuwar da yayi sai ya

shiga cikin wani yanayi na tunani game da hanyar da zai bi wajen

cika Alkawarin da ya dauka, 

To sai dai domin Allah ya saukaka

masa game da rantsuwar da yayi na yiwa matar sa bulala 100

kuma musamman idan akayi la'akari da irin hidimar da tayi masa

na tsawon lokacin daya dauka yana fama da rashin lafiya. 

Don haka sai aka canza masa hanyar da zaibi wajen cika wannan

ranstuwar da yayi, don haka aka umarce shi da ya tattara

zangarniyar alkama ko kuma dabino har guda 100 sai ya hada su

waje guda sai ya doke ta sau daya dashi kaga ke nan ya cika

ranstuwar da yayi kenan na yin mata bulala 100.

To sai dai saboda irin rawar da matar Annabi Ayuba (AS) ta taka wajen kula da shi a lokacin da yake fama da rashin

lafiya kila masu saurare zasu su so sanin sunan ta da kuma tarihin

ta koda a takaice ne, Ita dai Matar Annabi Ayuba (AS) sunan ta

Rahima diyar Ibrahim bin Yusuf bin Ya'aqub bin Ishaq bin Ibrahim

(AS). 

Kuma tana daga cikin matayen da akayi ishara game da sunayen su acikin Alkur'ani mai girma, ta na da ga cikin mataye manya masu martaba da daraja, ta kasance bata da na 2 wajen hakuri da tsarki da kame kai da kauna da juriya game da bala'in daya samu mijin ta na rashin lafiya da yayi fama dashi. 

Ita dai Rahima tana daga cikin Matan da irin su basu da yawa a duniya, musamman idan aka duba irin hakurin da tayi na tsawon lokaci

wajen jinyar mijinta da bashi da Lafiya da dukkan karfin da take

dashi, wanda abin da tayi ya zama abin koyi ne ga sauran matan

duniya. 

Kamar yadda yazo game da falalar ta da kuma irin matsayin da ta 

ke da shi mai Girma Allama Majlisi ya Rawaito daga Ibn Babawaihi cewa tun bayan da Bala'i yayi tsanani sosai akan

Annabi Ayuba (AS) ta kowanne bangare sai dukkan Al'umma da

sauran yan uwansa suka guje shi, amma matar sa Rahima tayi

hakurin cigaba da kasancewa tare dashi duk da halin da yake ciki,

bata cire tsammani ba wanda zai kai har ma ta guje shi saboda

halin da yake ciki ba. 

Don haka ne ma Shedan yayi mata Hassada da Kyashi game da wannan babbar Hidima da takeyiwa Annabin Allah kuma Mijin ta Ayuba (AS), don haka ne ma Shedan din ya zo inda take yace mata a she ke bakina daya daga cikin yayan Ya'akub ba? Amma me yasa kika sanya kanki zama cikin wannan Wahala da Bala'i, sai wannan baiwar Allah kuma malama mai hakuri da karfin zuciya ta bashi amsa da cewa haka Allah Madaukakin Sarki yaso ya

ganni, kuma wannan yana daga cikin ikon sa da kudurar sa ne

mabuwayi gagara misali, domin ya bamu sakamako mai girma

saboda Albarkacin sa. 

Wanda tun da fari ya bawa Annabi Ayuba (AS) dukiya da yaya, amma domin ya Jarabce mu kuma ya bamu lada babba sai ya amshe wannan Ni'imar daga gare mu, sai ta tamabaye shi cewa shin ka taba ganin wanda aka ba shi tumaki mai yawa kamar nashi kaga ashe dole ne mu gode ma Allah game da kyautar da ya yi mana a bangare guda kuma mu kara gode masa game da Jarabawar da yayi Mana, don haka ya hada mana abubuwa guda 2:

Yayi mana wadata da Ni'ima dole ne mu gode masa a kan haka,

kana ya Jarabcemu da Bala'i na rashin lafiya ya zama dole muyi

Hakuri da Juriya akan haka wanda babu wani abu da karfinmu zai

iya bamu face neman dacewa da taufiki daga Jalla mabuwayi

gagara Misali, don haka duk makircin da shedan ya kulla domin

ya Rudi Rahima Matar Annabi Ayuba (AS) bai ci nasara ba saboda

tsananin karfin Imanin ta, inda ta tsaya da karfin zuciya ta nuna

gwarzantaka wajen bashi amsoshi masu yanke Hanzari. 

Iban Abbas ya fadi cewa ruwayoyi sun nuna cewa bayan da Annabi Ayuba (AS) ya samu waraka sai Allah ya dawo masa da samartakar sa inda ya haifi ya'ya ye har guda 26 duk da yake dama kafin fara rashin

Lafiyar sa yana da yaya maza guda 7 da kuma yaya mata guda 7

wanda dukkan su sun koma ga Mahaliccin su, Amma daga bisani

Allah ya dawo masu da samartakar sa shi da matarsa inda suka

sake haihuwar 'ya'yaye masu yawa tare. 

Wannan Itace Rahima

Matar Annabi Ayuba (AS) , hakaki akwai darussa da dama da Mata

da Maza zasu iya dauka acikin rayuwar ta musamman hakuri da

tayi wajen Jiyyar Mijin ta, da kuma shi kanshi Annabi Ayuba (AS)

na hakurin da yayi akan rashin Lafiyar da aka Jarabce shi da ita,

wanda hakan ke nuna cewa hakika duk wanda yayi Hakuri zai kai

ga cimma nasara kamar yadda masu iya magana ke cewa mai

Hakuri yakan dafa dutse har ya sha roman sa idan wanda ke iza wuta

ya Jure. 

Allah Madaukakin sarki ya bamu ikon yin hakuri da kowane irin hali Muka Samu kawunanmu a ciki.


Article Translation in English Language.

InshaAllah, today we will bring you the story of Prophet Ayuba (AS), the way his life was and the kind of patience he had for many years regarding the trials that God the Almighty sent down to him due to illness. 

Prophet Job (AS) is one of the 25 Prophets of God that God mentioned in the Holy Qur'an. His name is mentioned 4 times in the Qur'an, in 4 chapters, in 4 verses. 

And his name Ayub is derived from Aba, Yub that is the one who was restored to health, happiness, wealth and children after they were accepted. 

Prophet Ayyub (A.S) was one of the sons of Prophet Ibrahim (AS) as historians have revealed his lineage where they show that Ayuba bin Amus bin Razij, bin Rum, bin Isa, bin Ishaq bin Ibrahim. And his mother is one of the brothers of Prophet Ludu bin Harran (A.S). 

But the readers will want to know where the real birthplace of Prophet Ayuba (AS) is. 

There was a dispute among historians about the right of his homeland, where others stated that he was born in the cities of Basana, Iwada, Jabiyya, located in the city of Sham in the city of Damascus, Syria, and he was born 3642 years after the descent of Prophet Adam (A.S) to the earth.

And he returned to God when he was 93 years old and his grave is on the peak of Jihaf, which is 80 miles from the border of Yemen and the town of Adnan. 

An author of the book of Balami's history said that Prophet Ayuba (AS) lived in a town called Basneh in the outskirts of the country of Sham, and spent 7 years worshiping and seeking closeness to God while continuing to call the Ummah to the true path of God's Oneness, but there were 3 people. They just believed in him. 

He was one of the Prophets whose lives were explained in detail in the Holy Qur'an. 

He used to sympathize with the orphans, the poor and the blind who had no one to take care of them, and he was famous in the town for welcoming guests and the homeless and treating them well.

Prophet Ayuba (AS) used to have a lot of wealth and he used to tend animals, where he had many animals and birds, and he had a large farms in which he cultivated plant, but after a long time, all the farms, property and the animals that he owned ran out, and he was tested with many tests, including severe illness, in which there was nothing left in his body except his heart and his tongue that he used to mention God, but his whole body was sick. 

But still he was patient during the time he was sick, and he never showed weakness or tiredness.


SHARE THIS

Author:

Etiam at libero iaculis, mollis justo non, blandit augue. Vestibulum sit amet sodales est, a lacinia ex. Suspendisse vel enim sagittis, volutpat sem eget, condimentum sem.

0 comments: